Shugabar sashin kula da Sinawa dake kasashen waje na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wu Xi, ta halarci wani taron karawa juna sani jiya Laraba a birnin Beijing, inda ta bayyana yadda gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin dawo da mutanenta daga Sudan.
Wu ta ce, a yayin da ake kokarin dawo da Sinawa gida daga Sudan, ma’aikatan ma’aikatar harkokin wajen Sin sun rika tuntubar masu kula da ayyukan dawo da Sinawan bayan kowane mintuna talatin, don tabbatar da tsaron su. Duk wani dan kasar Sin, an san daga inda yake da kuma lokacin da aka dawo da shi.
Wu ta kara da cewa, ba ‘yan asalin kasar kawai kasar Sin ta taimaka wajen dawo da su ba, har ma ta taimaka wa wasu ‘yan kasashen waje 231 daga Pakistan da Brazil da sauran kasashe 8 ficewa daga kasar ta Sudan. (Murtala Zhang)