Tun bayan rantsar da shi kan karagar mulki, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara sauye-sauye da garambawul ga tsarin shugabancinsa.
Shugaba Tinubu ya gudanar da sauye-sauye a cikin ma’aikatun domin farfado da tattalin arziki da inganta rayuwar talakawan Nijeriya, wanda a ciki ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN), Godwin Emefiele da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasaha (EFCC), Abdulrasheed Bawa bisa zarge-zargen da ake yi musa na amfani da ofisoshinsu wajen yin sama-da-fadi da makudan kudade, wanda tuni har hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tana gudanar da bincike a kan su.
A wannan makon ma, Shugaba Tinubu ya yi wa dukkan hafsosin tsaro ritayar dole tare da maye gurbinsa da sabbin fuskoki domin inganta sha’anin tsaron kasar nan. Haka kuma an maye gurbin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba.
Tinubu ya sauya sunan Nuhu Ribadu a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA). A makon jiya ne aka nada shi mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tsaro.
Nade-naden na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar. An kuma maye gurbin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Hameed Ali.
Tsohon kwamandan rundunar soji na ‘Operation Hadin Kai’, Manjo Janar C.G. Musa dan asalin Jihar Kaduna a yankin arewa maso yamma ya maye gurbin Janar Lucky Irabor a matsayin hafsan hafsoshin tsaro, yayin da Manjo Janar T. A. Lagbaja dan asalin Jihar Osun da ke yankin kudu maso yamma ya maye gurbin Laftanar Janar Faruk Yahaya a matsayin shugaban hafsan sojojin Nijeriya.
Hakazalika, Air Bice Marshal H. B. Abubakar daga Jihar Kano da ke yankin arewa maso yamma ya maye gurbin Air Marshal Oladayo Amao a matsayin babban hafsan hafsoshin sojin sama, yayin da Rear Admiral E. A. Ogalla daga Jihar Inugu a yankin kudu maso gabas ya maye gurbin Bice Admiral Awwal Gambo a matsayin hafsan hafsoshin ruwa.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya nada Manjo Janar EPA Undiandeye a matsayin shugaban hukumar leken asiri ta tsaro. Ya maye gurbin Manjo Janar S.A. Adebayo.
A bangare daya kuma, an nada mataimakin Sufeto Janar na ‘yansanda mai wakiltar shiyyar kudu maso yamma, Kayode Egbetokun, a matsayin mukaddashin babban sufeton ‘yansanda na kasa, inda ya maye gurbin Usman Baba, yayin da Adeniyi Adewale aka nada shi a matsayin mukaddashin Kwanturola Janar na Kwastam.
Sanarwar ta ce nadin shugabannin hafsoshin tsaro da da na Sufeto Janar na ‘yansanda da kuma Kwanturolan Hukumar Kwastam za su yi aiki a kan mukamansu har sai an tabbatar da su kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.
Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Kanar Adebisi Onasanya a matsayin kwamandan dakarun soji da Laftanar Kanar Moshood Abiodun Yusuf a matsayin kwamandan bataliya ta 7 da ke Asokoro a Abuja da Laftanar Kanal Auwalu Baba Inuwa a matsayin kwamandan bataliya ta 177 da ke Keffi a Jihar Nasarawa.
Sauran sun hada da Laftanar Kanar Mohammed J. Abdulkarim a matsayin kwamandan bataliya ta 102 da ke Suleja a Jihar Neja da Laftanar Kanal Olumide A. Akingbesote a matsayin kwamandan bataliya ta 176 da ke Gwagwalada a Abuja.
Hakazalika, shugaban ya amince da nadin wasu hafsoshin soji a fadar shugaban kasa.
Su ne: Manjo Isa Farouk Audu a matsayin kwamandan jami’an gidan gwamnati da Kyaftin Kazeem Olalekan Sunmonu a matsayin babban kwamandan na biyu na gidan gwamnati da Manjo Kamaru Koyejo Hamzat a matsayin kwamandan hukumar leken asiri ta soja ta Fadar shugaban kasa da Manjo TS Adeola a matsayin kwamandan makamai na gidan gwamnati da Laftanar A. Aminu a matsayin kwamanda na biyu mai kula da makamai na gidan gwamnati.
Haka kuma Tinubu ya hada Hadiza Bala Usman a matsayin mashawarciya ta musamman a bangaren tsare-tsare da Hannatu Musa Musawa a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin tattalin arziki da al’adu da Sanata Abdullahi Abubakar Gumel a matsayin babban mataimaki na musamman a bangaren harkokin majalisar dattawa da Hon Olarewaju Kunle Ibrahim a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin majalisar wakilai.
Ana sa ran Manjo Janar Christopher Gwabin Musa na makarantar tsaro ta sojin Nijeriya wanda aka haifa a Jihar Sakkwato a yankin arewa maso yamma a ranar 25 ga Disambar 1967, zai karbi ragamar mulki daga hannun Janar Lucky Irabor.
Musa ya yi makarantar firamare da sakandire a Sakkwato, duk da cewa ya fito ne daga karamar hukumar Zangon Kataf ta kudancin Kaduna.
Babban hafsan sojan ya shiga makarantar sojoji ta NDA a shekarar 1986, inda ya samu horon soji na tsawon shekaru biyar a lokacin da sojoji ke rike da madafun iko a kasar nan.
A cikin watan Satumban 1991, an ba shi mukamin laftanan na biyu a rundunar sojojin kasa, daya daga cikin sassan da suka fi wahalar a bangaren sojojin Nijeriya.
Kafin wannan sabon nadin nasa, a shekarar 2021, an sake tura shi ya zama kwamandan rundunar hadin gwiwa a arewa maso gabas ta ‘Operation Hadin Kai.
Sabon hafsan soji, Manjo Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ya shiga makarantar horas da sojoji ta Nijeriya a ranar 12 ga Satumbar 1987, a matsayin mamba na kwas na 39. An ba shi mukamin Laftanar na biyu a ranar 19 ga Satumbar 1992, a cikin rundunar sojojin Nijeriya.
An haife shi a Ilobu da ke karamar hukumar Irepodun a Jihar Osun a ranar 28 ga Fabrairun 1968, ya halarci makarantar firamare a kananan hukumar Osogbo tsakanin 1973 zuwa 1979, sannan kuma ya halarci makarantar ‘St Charles Grammar’ da ke Osogbo daga 1979 zuwa 1984.
Daga nan ya halarci kwalejin kimiyya da fasaha ta Ibadan daga 1984 zuwa 1986 kuma ya sami takardar shaida a makarantar yammacin Afirka. Kafin wannan sabon mukamin, shi ne GOC a shalkwatar dibishon na daya.
Sabon Hafsan Hafsoshin Sojan Sama
An haifi Air Bice Marshal Hassan Bala Abubakar a ranar 11 ga Satumbar 1970. Ya fito ne daga karamar hukumar Shanono a Jihar Kano. Ya shiga rundunar sojojin saman Nijeriya a matsayin mamba na 39 kuma an ba shi mukamin a ranar 19 ga Satumbar 1992.
Babban jami’in yana da digiri a fannin kimiyya daga makarantar horar da sojojin Nijeriya da ke Kaduna. Ya yi kwasa-kwasan horar da jiragen sama a makarantar horar da jiragen sama ta 301 da ke Kaduna. Ya kuma yi kwasa-kwasai da dama a cibiyar sojojin saman Nijeriya da makarantar soji ta Jaji.
Kafin sabon mukamin, ya rike mukamai da dama daga cikinsu akwai jami’in gudanarwa na injiniyoyi 16 a rundunar sojin sama da ke Makurdi da kwamandar gudanarwa na musamman ta 97 na matuka jirgin saman soji da ke Fatakwal.
Sabon hafsan hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Emmanuel Ogalla, wanda ya maye gurbin Bice Admiral Awwal Zubairu Gambo bayan ya shafe shekaru biyu yana ofis.
Ogalla ya fito ne daga karamar hukumar Igbo-Eze ta arewacin Jihar Inugu. Karamarsa ta yi iyaka da jihohin Kogi da kuma Benuwai.
Sabon babban sufetan ‘yansanda Egbetokun. An haife shi a ranar 4 ga Satumbar 1964, a kauyen Erinja da ke karamar hukumar Yewa ta kudu a Jihar Ogun.
Egbetokun ya yi digiri na farko a fannin lissafi a jami’ar Legas. Kafin ya shiga aikin ‘yansandan Nijeriya, ya karantar da ilimin lissafi a kwalejin fasaha ta Yaba da ke Legas.
Ya kuma sami digiri na biyu a fannin injiniya, ya yi difloma ta PGD a fannin tattalin arzikin man fetur a jami’ar Jihar Delta, sannan kuma ya yi MBA a Jami’ar Jihar Legas.
Egbetokun ya shiga aikin ‘yansandan Nijeriya ne a ranar 3 ga Maris, 1990, a matsayin mataimakin sufuritandan ‘yansanda na 16. Shi ne babban jami’in tsaro ga Tinubu lokacin da ya zama gwamnan Jihar Legas a shekarar 1999.
Matsalar tsaro ta dade tana ci wa kasar nan tuwo a kwarya, wanda wasu ke ganin bai kamata a samu matsalar ba duba da irin makudan kudade da ake ware wa bangaren tsaro a cikin kasafin kudi a duk shekara.
Idan dai za a iya tunawa, a jawabinsa na farko a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin cewa harkokin tsaro shi ne babban abin da gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali a kai.
Kwanaki uku da rantsar da shi, Tinubu ya gana da shugabannin hafsoshin tsaro wanda ya sallama a fadarsa da ke Abuja.
Ya shaida wa hafsoshin tsaron da aka kora a yanzu karkashin jagorancin babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor da su mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron kasar nan.
Wadanda suka halarci zaman sirrin sun hada da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya da babban hafsan sojin ruwa, Bice Admiral Awwal Gambo da shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Isiaka Amao da babban sufeton ‘yansanda, Usman Baba, wadanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada su kuma yanzu Tinubu ya sauke su.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kuma amince da rusa dukkanin hukumomin gwamnatin tarayya na ma’aikatu, hukumomi, cibiyoyi da kamfanonin gwamnatin tarayya nan take domin yin amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba su, da kuma maslahar al’umma.
Bayan daukar wannan mataki na rushe shugabanin hafsoshin tsaro da Shugaba Tinubu ya yi, al’ummar Nijeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu, musamman ma masana da masu sharhi na cikin gida da waje game da cewa ko wannan sauyi zai iya haifar da da mai ido a bangaren tsaro?
Da yake tsokaci kan lamarin a daren jiya, wani masani kan harkokin tsaro da leken asiri, Kabiru Adamu, ya bayyana nadin a matsayin an samu daidaito.
Adamu ya shawarci Tinubu da ya ci gaba da tabbatarwa tare da yin garambawul a bangaren tsaro da kuma wajen gudanar da harkokin gwamnati.
Ya ce, “Mutanen da Shugaba Tinubu ya nada ciki har da sabbin shugabannin hidima na da kyawawan abubuwan tarihi da suka hada da gogewar aiki a wuraren da ake samun kalubalanci tsaro kamar Kaduna da Borno.
“Wannan yana nuna cewa sun fahimci kalubalen tsaro a kasar. Akwai adalci a cikin nadin waje ya game dukkan bangarorin kasar nan.
“Akwai wasu mukamai a bangaren tsaro da har yanzu ba a nada ba, don haka muna fatan za a samu daidaiton jinsi ganin cewa babu wata mace a jerin sunayen.
“Domin a samu hadin kai a fannin tsaro, dole ne shugaban kasa ya kara aiwatar da gyare-gyare a bangaren tsaro da gudanar da harkokin mulki.
“Wannan zai ba da damar samar da cikakken tsaro da ceto tsarin dimokuradiyya da aiwatar da aiki yadda ya kamata.”
Ko wannan mataki zai iya magance matsalar tsaro da kasar nan ta dade tana fama da shi? Lokaci ne kadai zai iya tabbatar da haka.
‘Yan Nijeriya musamman ma ‘yan jam’iyyar APC abokan hulda na siyasa na wadanda suke kusa da sabuwar gwamnati sun fara kamun kafa yayin da aka rushe shugabannin hukumomi, saboda su samu mukamai kasancewa daga cikin shugabanninsu ko kuma ‘yan kwamitin na hukumomin da cibiyoyin da ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Wannan ya biyo bayan samun umurnin shugaban kasa na ba da izinin rushe shugabannin hukumomi da cibiyoyi da kamfanonin gwamnati tarayya wadanda tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada su mukaman.
Wannan ya nuna irin wasu gyare-gyaren da garanbawul da gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali a yanzu haka wajen tafiyar da ayyukan gwamnati. An samu labarin wasu mutane na ci gaba da kamun kafa a wurin na hannun daman Tinubu domin su kasance daga cikin wadanda za a ba mukaman shugabannin hukumomi da cibiyoyi da ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Wani babba daga fadar shugaban kasa ya yi bayanin cewar wasu na ta kai gwaro da mari da kuma tuntubar wadanda suka kamata domin cika wannan burin nasu na samun mukamai.
Shi al’amarin neman mukamai a hukumomi da kamfanonin gwamnati an fara yin hakan ne jim kadan da ya rage sauran ‘yan awonni a rushe shugabannin hukumomin, bayan da aka rushe hukumomin ne sai aka fara neman mukaman wadanda suke masu muhimmanci.
Sai dai ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya nuna cewa bai da masaniya kan al’amarin da ya faru, bayan kuma wadannan hukumomi suna karkashin kulawarsa ne.
Yayin da ofishin Sakataren gwamnatin tarayya ya nuna bai da masanaiya dangane da abin da yake faruwa kan kamun kafar da aka fara yi, akwai wadanda suka sa ido kan yadda al’amuran da suke faruwa, inda suka ce lalle an fara kamun kafar da wasu suka ce ba a fara ba.
Yadda wasu suka maida hankali kan neman mukaman da za a ba da a hukumomin gwamnatin tarayya hasashen wasu ya nuna hakan zai kara ba da haske kan tsare- tsaren gwamnati za a samu saukin aiwatar da su nan da shekaru masu zuwa.
Kamar yadda alkalumma suka nuna lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Buhari kan matakan da aka dauka masu ban sha’awa ne na raba mukaman tsakanin sashen Arewa da na Kudu, yayin da sashen Arewa ya samu mukamai 289 shi kuwa na Kudu ya samu 278.
LEADERSHIP ta samu tabbacin Shugaban kasa Tinubu ya shirya bayyana sunayen shugabannin hukumomin da kamfanoni na gwamnatin tarayya.
Da yake an bayyana rushe mukaman shugabannin hukumomin tsohon shugaban kasa ya kafa, wata majiyarmu ta bayanna wa wakilinmu cewa an dade da samun sunayen wadanda aka tura wa Sakaraen gwamnatin tarayya, George Akume ya fara aiki wadanda za a ba mukaman.
“Shugaban kasa shirye yake ya yi sauye-sauyen da ba za su yi wa wasu dadi ba, saboda ya san aikin da ma’aikacin gwamnati yake yi, bugu da kari kuma saunayen wadanda za a bai wa mukaman an samar da su ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya ne za a yi sanarwar,” in ji wata majiya mai tushe.
Da yake bayani kan jita-jitar da ake yadawa na rushe hukumomin, babban jami’i Shugaban kasa Tinubu idan yana bukatar cimma burinsa a bangaren tsaro, ya san abin da ya fi dacewa da shi, ya yi aiki da jami’an tsaro na bangarori daban-daban wadanda suka san yadda ake tafiyar da aikin sosai.
Ba laifi bane wajen rushe mukaman shugabannin hukumomin ba matsawar dai bai kauce wa yadda doka ta shimfida ba a cikin tsarin mulkin kasa.
Hakazalika, Shugaban kasa Tinubu ya umarci babban bankin kasa (CBN) da ya dakatar da biyan ma’aikatu, rassa da reshe-reshe (MDAs) na gwamnatin tarayya har zuwa yadda hali ya yi.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaida wa jaridar Tribune a makon jiya cewa, shugaban ya bayar da umarnin ne tun kafin ma ya dakatar da gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele wanda yanzu haka ke garkame a hannu hukumar DSS.
A cewar majiyar, umarnin na zuwa ne bayan da Tinubu ya shiga ofis domin tabbatar da gaskiya da ma’ana a cikin ma’aikatu tare da dakile kokarin sata da wawushe dukiyar al’ummar kasa da ke lalitar gwamnati.
Majiyar ta ce, a binciken da ake yi, babu wani da ba za a bincika ba idan bukatar hakan ta taso, a kan wannan matakin, ma’aikatu sun shiga takunkumin biyan wadanda suke binsu kudade domin babu wani kudin da ke zuwa daga CBN a halin yanzu.
Wani darakta janar na wata ma’aikatan gwamnatin tarayya ya tabbatar da wannan batun, inda ya ce, ma’aikatarsu ba ta da kudin ma da za ta ci gaba da gudanarwa.
A cewarsa, “Gwamnatin tarayya ta sanya takunkumi a kan CBN da ya daina biyan kudade ga ma’aikatu, yanzu haka ba mu tsammanin shigowar kudi daga ko’ina, ba mu da kudaden da za mu biya basukan da suke kanmu hatta tallukar da aka yi mana ma babu kudin da za mu biya su.
“Amma muna fatan komai zai daidaita nan kusa ba da jimawa ba,” ya shaida.
Wannan matakin na zuwa ne a yayin da Shugaban Tinubu ya dakatar da mataimakin daraktan da ke kula da biyan albashi ta tsarin asusu na musamman (IPPIS) da kuma wasu daga ofishin akanta janar na tarayya kan zargin matsalolin da ake samu a sashin biyan albashi.