Shugaban hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi (NDLEA), Buba Marwa ya tabatar da cewa tsauraren matakan da suke dauka kan yaki da ta’ammuli da muggan kwayoyi ya haifar da mai ido, domin a cikin watani 29 kacal hukumar ta damke masu ta’ammuli da muyagun kwayoyi su 31,675.
Hukumar ta NDLEA ta kara da cewa cikin 31,675 da aka kama, 5,147 an tabbatar da laifinsu kuma an yanke masu hukunci, yayin da hukumar ta kwace muggan kwayoyi da suke da nauyin miliyan 6.3 a tsawon wannan lokaci.
Ya kara da cewa wannan kokarin yana cikin hobbasan da hukumar ke yi don hana jama’a ta’ammuli miyagun kwayoyi wanda a yanzu ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma kuma yana barzana ga ci gaban tattalin arziki da su kansu masu amfani da kwayoyin da kuma iyalansu.
Sakataren hukumar NDLEA, Mista Shadrach Haruna wanda shi ne ya wakilcin shugaban hukumar ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin a lokacin taron manema labarai na hadin gwiwa gami da karin haske ga wakilin ofishin Majalisar Dinkin Duniya da yaki da shan miyagun kwayoyi karkashin jagorancin, Mista Oliber Stolpe, don shirin aikace-aikace game da ranar yaki da miyagun kwayoyi ta Duniya ta shekarar 2023.
A cewasa, “Babban taken bikin wannan shekarar shi ne, ‘mutane su daina nuna wariya ga masu ta’ammuli da muyagun kwayoyi tare da ba su kariya game da wannan yanayi da ake ciki a nan Nijeriya”.
“A cikin shekara 2 da rabi da suka gabata, mun yi kokari wajen tsaurara matakanmu wanda ya rage safarar miyagun kwayoyi a cikin al’umma. A cikin watanni 29 mun kama masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi 31,675 da suka hada da manyan dilolin kwaya 35 tare da samun nasarar yanke wa 5,147 hukunci da kuma sama da mutum 11 da a yanzu haka ake ci gaba da gudanar da shari’arsu a kotu, a yayin da masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi 23,725 aka shiryar da su tare da gyara dabi’unsu wanda mafi yawansu sun shiga cikin sana’o’i a cibiyoyinmu da muka kafa.
“Akalla kilogiram miliyan 6.3 na muggan kwayoyin muka kwace, a cikin kokarinmu na hana safara da rarraba wadannan miyagun kwayoyin. Mun samu nasarar lalata gonakin tabar wiwi mai fadin hekta 852.142 da lalata manyan dakunan harhada magunguna da suke sanya maye guda 3. Zan iya tabbatar maku da cewa ko a yanzu da muke magana, jami’an hukumar NDLEA suna can suna aiki ba dare ba rana don ganin an kawo karshen ta’ammuli da miyagun kwayoyi”.
Ya kuma tabbatar da cewa a yanzu safarar miyagun kwayoyi ya ragu matuka, wanda an sami nasarar haka ne sakamakon namijin kokarin da hukumar take yi tare da wayar da kan masu ta’ammuli da miyagun kwayoyin don ganin sun bari kwata-kwata a harshe daban-daban a kafafen sadarwa a Nijeriya.
A nasa jawabin, Mista Stolpe ya kara jaddada alfanun hadin kai tsakanin kasa da kasa a ayyukan kawar da aikata ta’ammuli da muggan kwayoyi, musamman wajen kawar da duk hanyoyin yada wadannan muggan ayyuka.
“Yana da kyau al’umma da hukumomin kula da lafiya a matakin farko su yi dukkan mai yiwuwa wajen samar da bayanai na wayar da kai game da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da nuna masu yadda illar da shan muggan kwayoyi ke yi wa mutane.
Mista Stolpe ya yaba wa ayyukan hukumar NDLEA wajen yaki da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da kuma safarar kwayoyin a Nijeriya.