A wannan makon masu karatu sun bayyana ra’yoyinsu ne game da tsarin bai wa dalibai bashin karatu da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya rattaba hannu a kai a kwanan baya.
Hassan Y. Balarabe
Dangane Da Bawa Dalibai Rancen Kudin Karatu, ga yadda na fahimci tsarin kamar haka:
- Karkashin dokar za a kafa Bankin Ilimi na Najeriya, wanda shi ne zai rika tsarawa da sa ido da kuma aiwatar da bayar da bashin karatun.
- Bisa tanadin sabuwar dokar, dalibi zai iya samun bashin ne ta hannun ma’aikatar ilimi ta kasar, kuma ba zai fara biyan bashin ba sai ya samu aiki bayan kammala karatu da kuma hidimar kasa ta shekara daya (NYSC).
- Dalibai za su iya neman bashin ta hanyar makarantun da suke, inda makarantun za su shige musu gaba.
- Za a tantance dalibi a ga ko ya cancanci karbar bashin.
- Dokar ba za ta amfani duk dalibin da zai yi karatu a wajen Najeriya ba, ko kuma mai karatu a makarantar da ba ta gwamnati ba.
Wanda Ya Cancanci Karbar Bashin.
- Kafin ka cancanci samun rancen sai da farko ka samu gurbin karatu a wata babbar makaranta ta jiha ko ta tarayya – walau jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha( polytechnic ) ko kwalejin ilimi ko kuma makarantar koyon san’ar hannu.
- Dole ne kudin da kake samu ko kuma iyayenka suke samu ya kasance kasa da naira dubu 500 a shekara.
- Dole ne dalibi ya gabatar da masu tsaya masa, akalla mutum biyu wadanda za su kasance ma’aikatan gwamnati da suka yi shekara 12 a aiki.
Dalibi zai iya gabatar da lauya wanda ya kai shekara 10 da aiki ko kuma wani ma’aikacin shari’a.
Idan dalibi a makarantar da ba ta gwamnati yake ba ba zai samu wannan rasnce ba. - Babu maganar wariya ko nuna bambanci ga wani dalibi bisa jinsi na mace ko namiji ko addini ko wata nakasa.
- Bashin zai kasance na biyan kudin makaranta ne kawai.
Wadanda Ba Za A Ba Bashin Ba.
- Idana ya kasance ka ci bashin Bankin Ilimin a baya kuma ka ki biya.
- Idan har wata makaranta ta tabaKo kuma wata kotu ta taba samunka da laifin rashin gaskiya ko zamba, to ba ka cikin wadanda za su ci moriyar tsarin.
- Idan an taba kama ka da laifin da ya danganci miyagun kwayoyi, wannan ma zai hana ka samun rancen.
- Idan har wani daga cikin mahaifanka, walau uwa ko uba ba su biya bashin da aka ba su ba na dalibtar to ba za a ba ka ba.
Yadda Za Ka Biya Bashin.
- Yana daga cikin aikin Bankin Ilimin ya rika bibiyar wanda aka bai wa bashin ya san lokacin da zai gama karatun, da aikin yi wa kasa hidima har zuwa samun aiki domin tabbatar da mutum ya fara biya a lokacin da ya dace.
- Bankin zai hada kai da inda kake aiki domin tabbatar da ana yankar kudin da ya kamata a rika sanya wa a asusun da ya ba ka bashin.
- Duk wanda aka bai wa bashin zai fara biya shekara biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC).
- Za a rinka yankar kashi 10 cikin dari na albashinka ana biya.
- Idan aikin kanka da kanka kake yi, wato ba a karkashin wani kake aikin ba, to gwamnati za ta rinka karbar kashi 10 cikin dari na yawan ribar da kake samu a duk wata, inda za ka rika kai kudin da kanka bankin; Kwana sittin da zamanka mai sana’ar kai za ka mika bayanan harkokin kasuwanci ko aikin naka, misali bankinka da wajen da kake zaune da abokan sana’ar da wadanda suke da hannun jari a ciki da sauran bayanai.
Idan ka ki biyan bashin za a iya yi maka hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari ko tarar naira dubu 500 ko kuma a hada wa mutum duka biyu.
Aunty Iyami
Shi kansa tsarin ba da bashin ba na Yaran talakawa ba ne bisa yadda na ga criteria na abin
Aliyu Sulaiman
Gaskiya tsarin ya yi. Sai dai matsalar yanda Dalibai za su biya bashin da suka daukarwa kansu.
Domin na ga tsarurruka masu kyau ma, ‘yan Nijeriya da suka samu bashin kawai suka mai da shi Ganima. Misali; Tradermoni, Marketmoni, Cobid-19. Duk an karbi bashin amma kuma ba biya ba.
Gani nake kamar wannan ma zai iya zama abin da wasu za su yi amfani da wata dama tasu dan kansu su kashe tsarin.
Abdul’aziz Mohammed Gombe
Kodayake komaii dai yana bukatar cikakken bayani game da tsarin domin ni a nawa bangaren muddun wannan tsarin zai haifar da karin kudin makaranta zuwa 400k ko 500k ban ga wani alfanu a cikin tsarin ba. Daga karshe muna kara kira ga gwamnati da ya kamata ta yi kokarin saukaka hanyar neman ilmi ga talakan kasar ba wai kawo wani tsarin da zai gallaza wa talakan ba. Allah yasa a dace ameen. Wannan tsarin ba na ra’ayin shi ko kadan.
Nuruddeen Muhammad Funtua
A gaskiya wannan ba karamin ci gaba ba ne gaskiya muna murna da wanna shiri Allah ya karo wa kasata Nijeriya ci gaba.
Mubarak Abubakar Saulawa
Idan har babu tsarin samar wa da daliban aikin yi na kai tsaye ko jarin koyon Sana’a da zarar sun kammala karatun. Da me za su biya bashin? A bar mu mu ci gaba da gungurawa kawai.
Muhd Bashir Sa’ad
Tabbas wannan kudiri ne mai kyau Fata dai da buri Allah ya sa wadanda aka yi wannan shiri domin su su amfana.
Shafa’atu Ado Shitu
Allah Ya sa dai ba ‘tuition fees’ za a lika wa dalibai ba.
Sa’adatu Saminu Kankia
Wallahi ya yi mana dadi, musamman mu da muke fama da karatun yara marayu, yanzu da rayuwa ta yi tsada, muna shan wahala, dan albashin ba ya isarmu mu yi hidimar gida mu yi ta sauran bukatun rayuwa, ga ta karatun, don haka ba mu iya tara kudin makaranta, Allah ya sa tsarin ya tabbata ta yanda saukin za ya iso gare mu.
Moha NG
Abun nan ya yi daidai ni ma makarantar zan koma dan na samu nima ‘loan’ din.
Saminu Dahiru Danbatta
Tsarin ya yi daidai Allah ya tabbatar da Alkhairi.
Nafisa Sadik
Gaskiya na ji dadi sosai, domin wannan tsarin ba karamin taimaka wa iyayye marasa karfi zai yi ba a fanin karatun ‘ya’yansu, domin wasu iyayyen na sha’awan yaransu su yi karatu, amma rashin wadata yana hana su tura yaran makarantar. Gaskiya muna godiya Mai girma shugaban kasa, Allah ya saka da alkhairi. Kuma Muna kira ga daliban da Allah zai sa su samu tallafin, da su yi kokari su yi amfani da damar dan su inganta rayuwarsu, kuma su rike alkawari dan ‘yan baya ma su mora.
Abubakar Saddeekue
To abun tambayar a nan shine ta yaya za a biya bayan gama karatun tun da gwamnatocin ba sa iya ba ma matasa aikin yi?