Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta yi watsi da sabon bukatar belin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, har sai an yanke masa hukunci kan tuhumar cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ke yi masa.
Kanu, wanda a halin yanzu yake fuskantar tuhume-tuhume 7, Lauyoyin sa a karkashin jagorancin SAN Cif Mike Ozekhome, acikin takardar korafi da suka rubutawa kotun, sun kalubalanci soke belin da kotun ta bayar a bayan nan na sakin Shugaban IPOB din.
Shugaban kungiyar ta IPOB ya shaida wa kotun cewa sabanin zargin da gwamnatin tarayyar ke yi masa na cewa ya gudu a baya lokacin da aka bashi beli, ya ce ya gudu ne domin tsira da ransa bayan da sojoji suka mamaye garinsa da ke Afaraukwu Ibeku da ke Umuahia a jihar Abia, lamarin da ya ce ya kai ga mutuwar mutane 28.
Mai shari’a Binta Nyako, ta ce ba ta gamsu da dalilan da shugaban kungiyar ta IPOB ya bayar ba na rashin gurfana a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar sa a wancan lokacin.
Don haka, Nyako tayi watsi da bukatar belin da aka gabatar mata a ranar Talata,