An tabbatar da hallaka mutum biyu da kuma raunata wasu mutum uku a wani sabon hari da ake zargin wasu ‘yan bindiga suka kai sansanin Fass da na Werengin da ke a karamar hukumar Riyom a Jihar Filato.
A cikin sanarwar da Dalyop Solomon Mwantiri jami’i a cibiyar da ke kula da wadanda tashe-tashen hankula ta kasa (ECCV) ya fitar, sanarwar ta bayyana cewa, anga Fulani a Wareng dauke da muggan makamai, inda suka yi kwanton bauna da nufin kashe duk wanda suka gani.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sintiri, Sun Yi Wa Mata Fyade A Katsina
- Za Mu Kawar Da Matsalar Tsaro A Nijeriya -Nuhu Ribadu
Solomon, ya bayyana cewa, harin ya auku ne da misalin karfe 4:43 na rana a yayin da Fulani l ke dauke da makaman suka zo wajen yin kiwo da shanunsu, inda suka kutsa sansanin na Wereng.
Ya ce, “mun damu matuka kan kai wannan sabon harin wanda Fulani suka shafe kusan awa daya, inda hakan ya janyo kashe wasu masu suna Chuwang Boyi da kuma Amos Dung, inda kuma wani mai suna Yohanna Pam da wani daya suka samu raunuka.
A wata sabuwa kuwa, wasu ‘yan bindiga sun yi wa wani mai suna Bulus Bakwet kwanton bauna a yankin Tahoss a karamar hukumar Riyom, inda suka shake shi har ya suma, inda aka yi gaggawar kai shi asibiti don a duba lafiyarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp