A ranar Lahadi da ta gabata ne kasar Sin ta mika wa kasar Masar wasu samfuran na’urorin tauraron dan Adam guda biyu na aikin tauraron dan Adam na MisrSat II. Lamarin da ya sa Masar ta zama kasa ta farko a Afirka da ke da karfin hadawa da gwada tauraron dan Adam.
A yayin bikin mika kayayyakin da aka gudanar a cibiyar binciken sararin samaniyar Masar dake kusa da sabon babban birnin kasar, ministar hadin gwiwar kasa da kasa ta Masar Rania Al-Mashat, ta gode wa kasar Sin bisa goyon baya da hadin gwiwa da ta yi da hukumar, da kasancewarta “babban abokiyar hulda” ta Masar.
Ta ce, cibiyar hada tauraron dan adam ta MisrSat II da cibiyar hada tauraron dan adam, da gwaje-gwaje (AIT) da kasar Sin ta samar sun kara habaka karfin kasar Masar a fannin binciken tauraron dan Adam, da raya kasa. Da aunawa da kuma kula da harkokin sararin samaniya, lamarin da ya sa Masar ta zama kasa ta farko a Afirka a fannin sararin samaniya. (Yahaya Babs)