Ana yin layya a ranar sallah wato goma ga watan Zul-hijja da kuma kwana biyu da suke biye da ita. Domin ganin haka duba Arrisãlatu [shafi na 100] da Attalƙīnu [shafi na 212] da Alma’ūnatu [1/486] da Almuƙaddimatul Mumahhidãti [1/337] da Alkãfi [shafi na 240] da Almudauwanatul Kubrã [1/614].
Duk wanda ya yi layya bayan waɗannan ranaku, wato ya yi a ranar 13 ga watan Zul-hijja, to layyarsa ba ta yi ba. Duba Alma’ūnatu [1/486] da Attalƙīnu [shafi na 212] da Attafrī’u [shafi na 38] da Alkãfi [shafi na 240].
Ana yin layya ne bayan an yi sallar idi bayan gabatar da huɗuba, liman ya yanka dabbarsa ko ya soke ta. Duba Alma’ūnatu [1/490] da Attalƙīnu [shafi na 213]
Idan mutum ya yi riga liman ya yanka abin layyarsa kafin a yi sallah da huɗuba ya yanka tasa, to layyarsa ba ta yi ba sai ya sake wata. Duba Arrisãlatu [shafi na 109] da Alkarãfi [shafi na 240] da Almudauwanatul Kubrã [1/610]
Mutanen da suke ƙauye za su yanka abin layyarsu idan limamin kusa da su ya yanka tasa. Duba Almudauwanatul Kubrã [1/612] da Arrisãlatu [shafi na [109] da Albyãnu Wat Tahsīlu [3/340] da Alma’ūnatu [1/490]
Yin layya a ranar sallah ya fi falala. Duba Attalƙīnu [shafi na 212]
Ana yin layya ne tun daga hantsi har zuwa fuduwar rana. Duba Almuƙaddimatul Mumahhidãti [1/337] Kuma duk wanda ya yanka layyarsa da dare, to ba ta yi ba. Duba Almudauwanatul Kubrã [1/614] da Arrisãlatu [shafi na 109] da da Sharhu Zarruƙ [1/372] da Alkãfi [shafi na 240].
Idan mutum ya iya yanka, to mustahabbi ne ya yanka layyarsa da kansa ko da kuwa mace ce ko ƙaramin yaro. Duba Arrisãlatu [shafi na 109] da Attalƙīnu [212] da Alma’ūnatu [1/486].
Makaruhi ne mutum ya sanya wani ya yanka masa dabbar layyarsa matuƙar yana da iko kuma babu wani uzuri da ya sha gabansa. Duba Aƙrabus Sãliki [shafi na 84] da Jawãhirul Iklil [1/221].
Idan za a yanka layya za a ce Bismillahi Allahu Akbar Rabbana takabbal minna. Duba Arrisãlatu [shafi na 110] mutum zai iya kara wa da cewa: Allahumma minka wa laka. Duba Aƙrabus Sãliki [shafi na 85].
Idan mutum ya manta bai ambaci sunan Allah ba to, za a ci naman idan kuma da gangan ya ƙi ambatar sunan Allah, to bai halatta a ci ba. Duba Arrisãlatu [shafi na 110]
Mu hadu a rubutu na 5
Nuhu Ubale Ibrahim
Abu Razina Paki