Da sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙai. Yabo da godiya da kirari da girmamawa sun tabbata ga Allah Shi kaɗai. Yabon Allah da amincinsa su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, shugaban na farko da na ƙarshe tare alayensa da sahabbansa baki-ɗaya.
Bayan haka:
Wannan rubutu ya ƙunshi bayani a kan layya a bisa fahimtar Mazhabar Imamu Maliku ɗan Anas, Imamu Daril Hijrati Allah ya ji ƙansa, watau Malikiyya. Na zaɓi rubutun ya zama a haka saboda Mazhabar Malikiyya ake bi a wannan yanki namu, tare da kuma ƙarfin hujjoji da Mazhabar take da shi.
- Layya Babbar Ibada: Yadda Ake Gudanar Da Ita Da Matsayinta A Musulunci
- Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 2
- Layya Babbar Ibada A Musulunci Na 3
Layya sunna ce mai Æ™arfi a Muslunci ga duk wanda ya samu iko, wannan ita ce magana mashahuriya a Malijiyya. Duba; Arrisãlatu [shafi na 107]da Attalƙīnu [shafi na 211] da Alma’Å«natu [1/484] da Addurarul Bahiyyati [shafi na 145] da Al’irshadu [shafi na 100].
Wannan sunnar mai Æ™arfi ta Æ™unshi namiji da mace waÉ—anda suke ‘ya’ya ba bayi ba. Duba ; Alkãfi [shafi na 236] da Assharhus SagÄ«r [2/339].
Manya da yara sunna ce mai Æ™arfi su yi layya matuÆ™ar suna da ikon yi. Duba Iziyya tare da Fathu Rabbil Bariyyati [shafi na 763] . Kuma yaro ko maraya ne zai iya neman majiÉ“incin al’amarinsa ya ya yi masa layya matuÆ™ar yana da wadatar yi. Duba; Sharhul Iziyya na SharnÅ«bi [142].
Saboda haka; layya ba sai mai aure ne yake yi ba, ibada ce mai girman gaske da É—imbin lada, samari da ‘yan mata da zawarawa da tuzurai za su iya yinta, haka nan macen da take a gidan aure za ta iya yi idan tana da sarari koda kuwa mijinta ya yi, domin neman lada a wurin Allah Ta’ala matuÆ™ar suna da iko. Layya tana daga cikin alamomi (sha’a’ir) na addinin Islama kuma tana da falalar gaske.
Layya ta fi ‘yanta wuya (‘yanta bawa) da sadaÆ™a falala saboda tana cikin Sha’a’ir na Muslunci. Duba; Aljawãhiruz Zakiyyati [shafi na 143] da Addurarul Bahiyyati [shafi na 145].
Wata Fa’ida: A cikin malaman Malikiyya akwai waÉ—anda suke ganin layya wajibi ce ga duk mai iko. Kuma wannan magana ita ce shahararren malami kuma Æ™wararre a Malikiyya mashahurin malami Farfesa Mansur Sokoto Allah ya zama gatansa ya rinjaryar kuma ya fi ganin ingancin ta. Duba Muhd Mansur Sokoto; Fathu Rabbil Bariyyati [shafi na 767].
Ana layya ne da jinsin dabbobi na ni’ima guda huÉ—u kamar haka:
1. Tumaki
2. Awaki
3. Shanu
4. Raƙuma.
Mu haÉ—u a rubuta na 2 don sanin shekarun dabbar da za a yi layya da ita.
Nuhu Ubale Ibrahim
ABU RAZINA PAKI
8/12/1442
Bugu Na 2