A ranar 22 ga watan Yuni, an kafa cibiyar raya al’adu da tattalin arziki da cinikayya ta Sin da Afrika, inda jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC ta jagoranta, inda ta sanya hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar a yankin rukunin masana’antun zamani dake Fuzhou.
Wannan shi ne karon farko da aka kafa cibiyar musayar al’adu da huldar tattalin arziki ta Afrika a kasar Sin.
A wannan rana kuma, aka bude yankin masana’antun zamani na Fuzhou, kuma aka gudanar da bikin sanya hannu kan aikin zuba jari na tattalin arzikin zamani.
Cibiyar raya al’adu da tattalin arzikin Sin da Afrika ne ta jagoranci sanya hannu.
Aries Chi Chiu CHEUNG, daraktan sashen Asiya na majalisar bunkasa ciniki da zuba jari ta kasa da kasa ta Kongo DRC, wanda ya jagoranci sanya hannun, ya bayyana cewa, cibiyar raya al’adu da tattalin arziki ta Sin da Afrika ne ta zabi kafa cibiyar a yankin Fuzhou, ana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Kongo (DRC), da fatan cibiyar raya al’adun tsakiyar Afrika za ta taimakawa Kinshasa wajen yayata wannan shiri, kana za ta hada kai da kasashen tsakiyar Afrika wajen daga matsayin huldar tattalin arzikin da musayar al’adu da cinikayya tsakanin Sin da Afrika. (Ahmad)