A ranar Juma’a ne kungiyar kwadago a Jihar Kano za ta yi taro kan matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauka na dakatar da biyan albashin ma’aikata 10,800 da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta yi.
Shugaban NLC na Kano, Kabiru Inuwa, ya shaida wa Leadership Hausa a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa kungiyar ta yi zamanta ne a ranar Talata, inda ta tattauna kan lamarin tare da sanya wani zama ranar Juma’a domin yanke hukunci kan lamarin.
- Shugaban INEC Ya Tafka Aika-Aika Fiye Da Emefiele, Ya Kamata A Kore Shi —Buba Galadima
- Zaman Lafiya Zai Bunkasa A Kaduna -Uba Sani
Inuwa ya shaida wa wakilinmu cewa, “Za mu yanke shawara ta karshe kan batun bayan wani taro a ranar Juma’a kuma za mu yanke duk wani kuduri da muka cimma ga jama’a.”
Leadership Hausa ta ruwaito a ranar Litinin din da ta gabata cewa Gwamnan jihar Kano mai ci ya umarci Akanta-Janar na jihar ya dakatar da biyan albashin ma’aikata 10,800 da tsohon gwamnan jihar, Ganduje ya dauka aiki kafin barin gwamatin.
Kafin ya karbi ragamar mulki, Yusuf ya zargi gwamnatin Ganduje da daukar ma’aikata sama da 10,800 ba bisa ka’ida ba.
A yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin, Akanta-Janar Abdulkadir Abdusalam, ya ce gwamnan ya umarci ofishinsa da ya cire ma’aikatan daga tsarin albashin ma’aikata a jihar.
Babban Akanta-Janar ya ce ofishinsa zai gudanar da bincike don tabbatar da sahihancin ayyukan ma’aikatan da abin ya shafa domin cire wadanda aka dauka ba bisa ka’ida ba.