Shawarar mu ga gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif Abba Gida-Gida ita ce a yi wa manoman Kano sabon tsarin bunkasa noma a zamanin mulkinsa wanda manoman ba za su taba mantawa da shi ba kamar aikin marigayi Alhaji Audu Bako.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Sarkin Noman Masarautar Gaya, Alhaji Ibrahim Yakubu Tagahu a zantawarsa da wakilinmu.
Ya ci gaba da cewa, “domin Kano dai na da ginshikai, kamar Ilimi, Karatu, Noma, Sarauta, Kasuwanci, kuma akasarin mutanan Kano manoma ne da `yan kasuwa kuma yanzu haka an kiyasta Kano tana da albarkar yawan jama`a da suka kai kimanin Miliyan 20 a kiyasi, duk da rabon Kano da kidayar jama`a tun shekarar 2006 yau kimani shekara 17 kenan wanda ina ganin cewa a kiyasin muna da manoma a Kano za su haura miliyan 15 wanda ka ga sunfi yawan mutanan wasu kasashe da dama a duniya a mahangar mu ta manoma da mu ke zama a yankunan karkara.
Bayan ya yi murnar kammala zaban shugaban kasa da na `yan majalisar dattawa da na wakilai na tarayya da na jihohi da kuma gwamnoni lafiya a Nijeriya, Alhaji Ibrahim ya ce abin da yake kara faranta musu rai game da zaben shi ne, “a ciki ne aka zabi mai girma gwamnan Jahar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif Abba Gida- Gida wanda kuma danmu ne kuma jikanmu ne idan aka yi la`akari da tarihin sabon gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif mai alaka ko tarihi da masarautar Gaya da ta Kano baki daya.”
Ya kara da cewa, “Babu shakka kowa ya san Kano kasa ce mai albarkar noma da fadin kasa mai karbar shuka kowa ne iri na duniya a kyakkyawan zato na idan aka shuka shi a Kano za yi bisa la`akari da shuke-shuken da mu ke na rani da na damina tun daga kan Dawa, Gero, Masara, Shinkafa, Dauro, Maiwa, Wake, Gyada, Waken suya, Accha,Alkama a noman rani, da sauran nau`o`i iri-iri na kayan abinci mai kwaya.
“Haka kuma a Kano ana noman gyada wanda Kano na noma gyada a kalla 60 cikin 100 na noman gyada a Nijeriya muna noman auduga duk a noman damuna a Kano a na noman Rogo, Makani, Gwaza, haka a na noman dankali a Kano, ana noma Albasa, yakuwa, Doborodo, Rama, Zogale, da sauransu haka a Kano ne ake noman rake noman takanda, haka a laiyahu da dai sauransu wanda wadannan abubuwa idan aka samu tsari na gwamnatin Kano ko ta tarayya a gona daya za a iya samar wa miliyoyin matasa aikin yi wanda za a dogara da kai ba tare da ragaita zuwa ofis ko kamfanoni neman aiki ba. Wannan kuma ba zai yiwu ba sai da kyakkawan tsari na gwamnatin Kano ta Abba Gida-Gida koma ta gwamnatin tarayya karkashin Shugaban Kasa Ahmad Bola Tunubu.
Da ya juya kan matsalolin manoman Kano kuwa, Sarkin Noman na Gaya ya ce, “Kadan daga cikin Matsalolin manoman Kano da mu ke son a kawo mana kyakkyawan tsari na tallafa mana akwai karancin motocin noma da kayan aiki na zamani karancin guraran noman rani bisa la`akari da yadda Kano ta ke da dam-dam wato madatsun ruwa wanda aka gina su tun zamanin marigayi Audu Bako tun lokacin da Kano ta zama jiha a shekarar 1966 suke wanda suna da bukatar a yashe su a tsattsaga su domin fadada gurin noma ga dimbin matasanmu na Kano.
“Haka tsarin tallafa wa manoma duk lokacin da gwamnatin Abba Gida-Gida za ta yi ko ta Tunubu, wajibi ne a samo a halin abun kamar manoma, da shugabannin su da sarakunan su, da kuma sarakuna iyayen al`umma da sauran shugaban ni wanda al`umma ke ganin kimarsu amma sanya siyasa wajan raba tallafin noma mu dai manoma na gaskiya ba ma amfana da wannan tsari kuma yau manoma na fama da tsadar taki, tsadar irin, tsadar maganin ciyawa, da sauran kayayyaki da manoma su ke amfani da su yau sun yi tsada wanda a neman kyakkyawan tsari na tallafa wa manoman Kano dan bunkasawa.
“Haka zalika shawarar mu duk wanda za a bawa kwamishina na ma`aikatar gona da sauran shugabanci na KASCO Da KANARDA da sauran cibiyoyin bunkasa noma a Kano a bawa wanda ya san harkar, mai kishin harkar, hakan zai taimaka wa mu manoma haka kuma mu na yaba wa sabon gwamnan Kano kan kishinsa na ilimi, lafiya, tattalin arziki, kasuwanci, ruwan sha, Taswiyyarar Kano, Tsaro, Samar da aikin yi ga matasa da dai sauransu kan yadda muka ga ya himmatu da hawansa gwamnan Kano.” In ji shi.
A karshe, sarkin noman masarautar noman Gaya Alhaji Ibrahim Yakubu Tagahu, ya ce “a madadan sarkin Gaya Dr. Ibrahim Abdulkadir muna yi wa Alhazan bana da suka sauke farali da mu wadanda muka yi Sallar Layya, muna yi wa masarautar Gaya, masarautar Kano, da Jihar Kano da Nijeriya fatan samun wadataccan tsaro da zaman lafiyar al`ummar Nijeriya baki daya.” Ya bayyana.