Shugaba Tinubu ya yi kira ga alhazan Nijeriya da suka je aikin hajjin bana a kasar Saudiyya da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa abu mai muhimmaci a aikin Hajji shi ne hakuri da sadaukarwa a cikin wahalhalu.
Jakadan Nijeriya a kasar Saudiyya, Ambasada Yahaya Lawal, ne ya isar da sakon shugaban ga alhazan Nijeriya yayin ziyarar da ya kai tantin maniyyatan a Mina a Alhamis.
- Mahajjatan Nijeriya Sun Yi Wa Ƙasa Addu’o’i Na Musamman A Filin Arfa
- Mahajjata Sama Da Miliyan 2 Ne Za Su Yi Aikin Hajjin Bana
Wakilin Nijeriya wanda ya samu rakiyar takwaransa na kasar Sudan, Ambasada Safiu Olaniyan, shugaban hukumar alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, da kwamishinoninsa da manyan jami’an hukumar NAHCON, ya bukaci alhazan Nijeriya da su ci gaba da gudanar da aikin hajjinsu na bana cikin tsari da zama jakadu nagari na kasarsu a lokacin da suke kasa mai tsarki.
Shugaba Tinubu ya kuma shawarci mahajjatan da cewa, maimakon yin gunaguni game da kalubalen da suke fuskanta, ya kamata su mai da hankali kan muhimmancin tafiya kasa mai tsarki tare da mayar da hankali wajen yi wa Nijeriya addu’a, yana mai cewa kasar na bukatar addu’o’insu don shawo kan kalubalenta.
“Yanzu haka an sanar da shugaban kasar kan irin kyawawan dabi’un da kuka nuna kuma yana fatan ku ci gaba da wakiltar Nijeriya da kyau a kasa mai tsarki. Sannan ku sanya Nijeriya cikin addu’o’in ku, mun san kalubalen da kasarmu ke fuskanta kuma yana da muhimmanci ku yi amfani da wannan dama ta musamman wajen yin addu’a ta musamman don ci gaban Nijeriya, zaman lafiya, kwanciyar hankali da walwala ga ‘Yan Nijeriya.
“Muna godiya da goyon bayanku, kuma muna mika godiyarku ga shugaban hukumar NAHCON bisa yadda ya samar da shugabanci na gari, muna fatan shugabannin su ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da suke yi har sai dukkan alhazai sun dawo gida lafiya.” Cewar Lawal.
Tun da farko, shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya ce makasudin ziyarar ita ce ziyarar mahajjata tare da ganin abubuwan da suka faru a aikin Hajji a wurare masu tsarki musamman a Mina, Arafat. da Muzdalifa da ayyukan Hajji baki daya.