Har zuwa yanzu dai tsugume ba ta kare ba kan shugabancin majalisar kasa ta 10 yayin da wasu fusatattun Sanatoci suka kammala shirye-shiryen garzayawa Kotu domin kalubalantar nasarar da Godswill Akpabio ya samu a matsayin shugaban majalisar dattawa.
Kamar yadda LEADERSHIP ta gano cewa, ‘Yan majalisar sun nuna rashin gamsuwarsu kan kuri’un da aka yi amfani da su a wajen zaben shugaban majalisar dattawan da zargin an tabka magudi a zaben.
- Sanata Akpabio Ya Lashe Zaben Shugaban Majalisar Dattawa
- An Rantsar Da Akpabio A Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa Na 13
An kuma gano bayan zaben na majalisar dattawa ta 10, wasu Sanatoci na shirin yin tutsu ga jam’iyyar APC da barazanar ficewa daga cikinta.
Wata majiya daga majalisar ta shaida wa wakilinmu cewa Sanatoci 22 sun gama shirin sauya sheka zuwa wasu Jam’iyyun siyasa, ta yadda ‘yan adawa za su samu rinjaye a zauren majalisar.
Muddin wannan shirin ya tabbata, Jam’iyyun adawa za su samu mambobi 72 (Sanatoci) yayin da kuma APC za ta samu ragowar Sanatoci 37 kacal.
Sai dai kuma tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya karyata zargin da wasu abokan aikinsa sanatoci suka yi, tare da cewa ba wasa Sanatocin suka yi ba a ranar 13 ga watan Yuni da suka zabi Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa.
An gano Kalu wani faifayin bidiyo, ya ce, “A zahirin gaskiya zaben majalisar dattawa ya gudana bisa inganci. Sanata Akpabio ya ci zabensa. An yi bisa inganci kuma sahihin zabe.”
Kalu ya ce, ba a taba yin majalisa biyu ba, majalisa daya ce kuma sun riga sun kafata a ranar 13 ga watan Yuni tare da zaben shugaba da mataimaki.
To sai dai Sanatocin da suka zanta da wakilinmu sun yi watsi da ikirarin Kalu, suna masu hakikancewa kan ba za su bari sabon shugaban majalisar ya kammala wa’adinsa ba.
Wasu Sanatoci biyu daga arewa maso gabas masu ra’ayi irin fusatattun Sanatocin, sun ce, an malkwada zaben ne kawai domin a dakile takarar Sanata Abdul’aziz Yari.
Daya daga cikin Sanatocin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, “Duk da an yi zabe har ma Akpabio ya samu nasara, amma akwai tulin ayoyin tambaya a kasa.