A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasika mai kunshe da sakon taya murnar bude taro na 3, na musaya da koyi da juna tsakanin mabanbantan wayewar kai, wanda kuma shi ne taron dandalin farko na kasa da kasa na masana al’adun kasar Sin.
A cikin wasikar ta sa, Xi Jinping ya ce cikin tsawon tarihin rayuwar bil adama, al’ummu daban daban sun kirkiri salon wayewar kai mai nasaba da halayen su na musamman da alamun su. Kaza lika, musaya da koyi da juna tsakanin mabanbantan wayewar kai za su samar da jagoranci ga bil adama, wajen warware kalubalen da ake fuskanta, tare da samar da ci gaban bai daya.
Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin a shirye take ta yi aiki da daukacin sassa, wajen ingiza akidun bai daya na daukacin bil adama, ciki har da zaman lafiya da ci gaba da daidaito da adalci da dimokaradiyya da kuma ‘yancin kai, tare da aiwatar da shawarar wayewar kan al’ummun kasa da kasa, da yin aiki tare wajen ingiza wayewar kan dan adam. (Saminu Alhassan)