Wasu matan aure a birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa sun hakura da amfani da tumaturi wajen yin miya sakamakon tsananin tsadar da ya yi.
Matan sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), a ranar Lahadi cewa sun koma yin nau’o’in miya da Gauta da kuma Karas.
- Matsalar Tsaro Kalubale Ne Ga Samar Da Abinci -Bafarawa
- Tinubu Ya Gana Da Tawagar Kamfanin Man Fetur Na Shell
Sun ce Gauta yana yin daidai a ko wacce irin miya kamar yadda tumaturi ke yi.
Sauran kuma sun ce sun koma yin miya da Kabewa da Gwanda wajen yin nau’o’in miya daban-daban.
Matan sun ce duk da cewa shinkafa da miyar dage-dage shi ne abincin da su ka fi ci kuma su ka fi samun gamsuwa a yau da kullum, amma tsadar tumatur6 ta tilasta musu amfani da Gauta wajen yin miyar ta dage-dage su hada da shinkafa.