Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a (JAMB) ta haramtawa wata mai suna, Mmesoma Ejikeme, dalibar da ake zargi da fitar da sakamakon jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) zana jarrabawar har tsawon shekaru uku.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da shugaban hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, ya fitar a ranar Lahadi.
- Abbas Ya Sanar Da Manyan Shugabannin Majalisar Wakilai
- Akpabio Ya Nada Bamidele, Ndume, Umahi Da Asiru Manyan Mukamai A Majalisar Dattawa
Hukumar wadda ta gano samamakon jarabawar da Mmesoma ta buga na bogi a ranar Lahadi, ta nanata cewa, tuni ta dakatar da sakamakon dalibar.
JAMB ta kuma bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, ba a yi mata kutse a cikin manhajarta, ta adana sakamakon jarrabawar ba musamman ganin yadda wasu daliban suka yi kwafin sakamakon jarrabawar na bogi ba da wata mai suna na Asimiyu Mariam Omobolanle wadda ta zauna zana jararrabawar ta UTME a 2021, har ta samu makin da ya kai 138.
A cewar hukumar, “Za mu ci gaba da kare mutuncinmu, muna kuma son mu kara nanata bayaninmu na baya cewa, sakamakon na UTME da dalibar da ta gabatar, na cewa ta samu maki 138 a jarabawar UTME ta 2021 na bogi ne.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna son mu bayyana cewa, ita kanta Mmesoma ta bayyana hakikanin asalin wadda ke da sakamakon jarrabawar wanda ta ke ikirarin, inda ake da sakamakon ya bayyana asalin wadda ke da sakamakon tun kafin ta bayyana sakamakon.
Hukumar ta kuma shawarci al’ummar gari da su yi kokari su kwafi tsarin QR na shaidar sakamakon jarabawar don su gane wa idanunsu asalin wanda ya mallaki sakamakon kafin a yi na boginsa.
A cewar sanarwar, “shin ta ya za a ce, daga cikin daliban da suka zauna zana jarabawar UTME a 2023 a ce Ejikeme Mmesoma kadai ce ta iya bayyana sakamakonta.
Hukumar ta ce, ba wannan ne lokaci na farko da irin wannan ta taba faruwa da hukumar ba, inda ta tunasar da al’ummar kasar nan cewa, a lokutan baya an kai karar hukumar a gaban kotu, inda daga baya su kansu lauyoyin suka nemi yafiyar hukumar kan tsayawar da suka yi wa wadanda suka shigar da hukumar karar a gaban kotu.
Sanarwar ta kara da cewa, wani abin takaicin shi ne, yadda wasu suka sa son rai wajen bai wa Ejikeme kariya, inda sanarwar ta ce, ya kamata irin wadannan mutane su sake yin tunani.