Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta zayyana jihohi 14 da yankuna 31 da ka iya fuskantar mamakon ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliya daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Ibrahim Farinloye, Kodinetan NEMA, da me ofishin hukunar a Jihar Legas.
- Kotu Ta Tabbatar Da Korar Goje Daga Jami’yyar APC
- INEC Za Ta Gurfanar Da Wadanda Ake Zargi Da Aikata Laifukan Zabe
Farinloye ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihohin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya lissafa jihohin da yankunan kamar haka:
Filato: Langtang da Shendam
Kano: Sumaila da Tudun Wada
Sakkwato: Shagari, Goronyo da Silame
Delta: Okwe
Kaduna: Kachia
Akwa Ibom: Upenekang
Adamawa: Mubi, Demsa, Song, Mayo-belwa, Jimeta da Yola
Katsina: Katsina, Jibia, Kaita da Bindawa
Kebbi: Wara, Yelwa da Gwandu
Zamfara: Shinkafi da Gummi
Borno: Briyel
Jigawa: Gwaram
Kwara: Jebba
Neja: Mashegu da Kontagora
Farinloye ya gode wa Hukumar Hasashen Ruwan Sama (FEWS) da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya Abuja bisa bayyana bayanan daminar bana akan lokaci.