Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta ce binciken kwakwaf din da aka gudanar ya nuna bidiyon Dalar da ake zargin tsohon gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje da karbar na goro gaskiya ne.
A shekara ta 2018 ce dai jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu jerin faya-fayan bidiyo da suka nuna Ganduje yana karbar Dalolin Amurka, abin da aka yi zargin cin hanci ne daga wasu ’yan kwangila.
- Majalisa Ta Dakatar Da JAMB Daga Hukunta Dalibar Da Ta Yi Sakamakon Bogi
- Mene Ne Makomar SCO? Bari Mu Ji Ra’Ayin Shugban Kasar Sin
Amma tsohon Gwamnan ya sha karyata hakan, inda ya ce hada su aka yi kawai domin a bata masa suna.
Sai dai yayin da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa na yini daya kan yaki da rashawa a Jihar Kano ranar Laraba, Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya tabbatar da ingancin bidiyon.
Ya ce tun lokacin da aka fitar da su, mutane da dama ke kalubalantarsa da ya bayyana sahihancinsu ko akasin haka.
Ya kuma ce hukumarsa ta fara binciken bidiyon ne tun a shekara ta 2018, amma ba ta iya ci gaba ba a lokacin, saboda tsohon Gwamnan na kan kujerarsa, kuma yana da rigar kariya.
A kwanakin baya ne dai Muhuyi ya lashi takobin ci gaba da binciken bidiyon, ’yan kwanaki bayan sabon Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi kan kujerar shugabancin hukumar.