An shirga tirka-tirka kan soke sakamakon jarrabawar JAMB ta wata dalibar sakandaren ‘yan mata ta Anglican da ke yankin Nnewi, a Jihar Anambra, Ejikeme Mmesoma da Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a (JAMB), ta yi a makon nan. Biyo bayan zargin da ake mata na aringizon makin jarrabawar daga 249 zuwa 362, tare da ayyana kanta matsayin wadda ta fi kowane dalibi samun maki a jarabawar ta 2023.
Masana na wa lamarin kallon koma baya kuma babban kalubale a harkokin ilimi a kasar nan.
- Hajji 2023, Wata Hajiya ‘Yar Jihar Kano Ta Rasu A Makkah
- Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Kasashen Afirka
Hukumar ta soke sakamakon jarrabawar dalibar tare da dakatar da ita daga sake rubuta sabuwa na tsawon shekara uku da kuma barazanar gurfanar da ita a gaban kotu.
A wani labarin kuma, Hukumar ta JAMB ta gano karin wani dalibi dan asalin Jihar Kaduna, Atung Gerald, wanda kwata-kwata bai ma rubuta jarrabawar ba amma ya yi ikirarin samun maki 380.
Mai magana da yawun hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ya ce masu aringizon jarrabawar suna yi ne domin damfara, inda tuni ma har Ejikeme ta samu kyautar naira miliyan uku (N3m) a matsayin tallafin karatu daga babban dan kasuwar nan na Jihar Anambra, Innocent Chukuma.
Da farko gwamnatin jihar Anambra ta shirya karrama dalibar amma daga bisani ta dakatar sakamakon wani babban jami’inta ya kira hukumar JAMB don tabbatar da ikirarinta dalibar, inda hukumar ta bayyana cewa Ejikeme Joy Mmesoma ta samu maki 249 ne sabanin 362 da ta yi ikirari. Haka nan JAMB da bayyana Umeh Nkechinyere, a matsayin wanda ya samu maki 360 a jarrabawar ta 2023.
…Daliban Da Suka Yi Zarra A Jarrabawar Cikin Shekara 10
Wani binciken da Mujallar Tattalin arziki ta gudanar a kan sakamakon jarrabawar JAMB tsakanin shekarar 2013 zuwa 2022; ya bayyana cewa dalibai 56 ne suka samu makin da yah aura 290 a cikin shekara 10.
Daga cikin dalibai 56 wadanda suka fi yawan maki a cikin shekaru 10, dalibai 16 suka sami maki 290 zuwa 339, yayin da dalibai 40 suka samu tsakanin 340 zuwa 363.
A 2013 da 2014, babu wani dalibin da ya samu maki 300, wanda binciken ya nuna mafi girman maki a cikin shekarun biyu shi ne wanda ya samu maki 299.
Binciken ya kara gano cewa dalibai hudu ne kawai suka sami maki sama da 360 a cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da wani dalibi haifaffen jihar Anambra, Maduafokwa Agnes, ya zama gwarzon UTME inda ya samu maki 365 a shekarar 2020. Sannan dan asalin jihar Borno, Galadima Zakari, ya zama na biyu mafi samun maki yayin da ya rubuta jarrabawar a 2018 ya samu maki 364.
…Masani Ya Tona Asirin Lamarin
Ganin yadda lamarin ya tayar da kura, LEADERSHIP Hausa ta bi diddigin hanyoyin da ake iya amfani da su wajen datsar bayanai ko kuma sauya sakamakon jarrabawar ta JAMB inda wakilinmu ya tattauna da wani masanin Kimiyya da Fasaha daga Jihar Kano, Abubakar SD kan siddabarun da ake amfani da shi wurin yin kutse tare da sauya sakamakon jarrabawar JAMB.
Ya bayyana cewar akwai wasu hanyoyi uku da za a iya bi wajen datsar bayanai ko sauya sakamakon jarabawa. “Daga cikin hanyoyi ukun, na farko yana da matukar wahala a ce wani ya aikata shi, tun da kawo yanzu tun bayan kafa hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ba a taba samun rahoton cewar wani ya datsi bayananta ba.
“Hanya ta farkon ita ce hanyar kutse, wato a bi ta bayan fage ta hanyar da ita JAMB din ba ta sani ba a shiga a sauya sakamakon jarabawar a shafinta na Intanet. Wannan har yau ba a taba samun labarin wanda ya yi ba. Amma za a iya cewa ke nan za a iya yi, watakila tunda ita harkar ta tsaro Dan’adam ne yake yi kuma Dan’adam ne zai iya karyawa.
“Hanya ta biyu, wadda take ba ta kai wannan wahala ba, amma ita ma tana da matukar wahalar gaske. Ita ce wadda ake rade-radin cewa ana yi, ma’ana ka samu a yi ‘yar gida. Ka samu wani ma’aikacin wannan hukuma ko kuma wani wanda yake da bayanai na wannan hukuma ko kwamfutar wannan hukuma wato fannin da suke dora sakamakon jarrabawarsu, shi wannan jami’i da ka samu ka hada kai da shi, walau ka biya shi kudi ko kuma ku kuka san yadda kuka cimma yarjejeniya, ya je ya canja maka wannan sakamako ka ba shi lambarka ta wannan jarrabawa ta JAMB shi kuma ya canja maka sakamakon.
“Kamar dai yadda ake yi a wasu makarantu musamman na gaba da sakandare, ka je ka bai wa wani ya dauko takardarka ya duba lambarka ya kara maka maki ko ya rage maka maki da sauransu.
“Wannan hanyar ana rade-radin cewa ana amfani da ita ko kuma an yi amfani da ita kuma tana da sauki ba ta kai hanyar farko wahalar yin kutse don a sauya sakamakon jarrabawar share fagen shiga Jami’a, wato JAMB ba kenan.
“Hanya ta uku kuma ta karshe wacce a masaniyata nake ganin za a iya bi domin sauya wannan sakamako na jarrabawar JAMB, wanda ta fi kowane sauki a cikin wadannan ukun kuma ta fi kowane saukin tonuwar asiri idan ka yi shi a gano ka, shi ne abin da ake cewa ‘manual changes’ wato ka je ka canja sakamakon jarabawar kai da kanka ko hannunka ko ka samu wani ya canja maka shi da kwamfuta dinsa ta dakinsa.
“Ta hanyar amfani da wasu manhajoji masu saukin ganewa masu saukin samu, irin su ‘Microsoft Office’ ko kuma ‘Adobe Photoshop’, irin wadannan da ma wasu manhajojin masu arha duk za a iya amfani da su a yi ‘manual changes’ na sakamakon jarrabawar JAMB kuma sun fi saukin ganewa asiri ya tonu.”
A ganin masanin, dalibar da aka soke jarrabawarta, Ejikeme watakila ta yi amfani ne da hanya ta uku, yana mai cewa, “Daliba Ejikeme wadda aka samu wannan yanayi na sauya sakamakon jarrabawa na irin wannan na karshen ne wato ‘manual changes’ kenan wanda za a iya zuwa a yi amfani da ita wannan kwamfuta a canja sakamakon ko ta amfani da wasu kananan manhajojin.
“Hanyar da za a bi a gane cewa mutum ya yi wannan, idan ya yi amfani da wannan na karshen shi ne, a jikin shi sakamakon jarrabawar JAMB akwai matakan tsaro da ita hukumar ta saka, daga ciki akwai ‘Barcode’.
“Barcode wani abu ne da ake haskawa wanda idan aka haska zai kawo maka ainahin sakamakon jarrabawar da aka dora a shafin hukumar, ka ga ke nan idan wani ya je ya canja sakamakon jarrabawa, misali yana Jihar Legas kai da kake Jihar Jigawa idan ka haska wannan sakamakon kai tsaye za ka ga ainahin sakamakon da hukumar ta fitar.
“Ka ga kenan idan a takarda sakamakon ya canja, kai kuma ka haska ta Intanet za ka samu ainahin sakamakon wanda za ka ga ya sha bamban da wanda aka kawo maka, ka ga asiri ya tonu. Bayan haka ana iya gano wasu abubuwa da ba daidai ba, musamman ta hanyar sake fitar da sakamakon jarrabawar JAMB din tun da an riga an yi gyara a jiki,” a cewarsa.
…Martanin Wasu Malaman Jami’o’i
Wani malami a Tsangayar Koyar da Tattalin Arziki da Ci Gaba a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashu’a, Dr. Habibu Muhammed ya bayyana wannan al’amarin a matsayin abin kokawa dangane da ci gaban ilimin jami’o’i irin yadda wasu dalibai kan yi kuruciyar bera a kokarinsu na shiga Jami’a.
Ya ce, “Wannan ‘yar manuniya ce bisa ga halin da ake ciki na koma baya a kasar nan, ya dace Hukumar kula da tsara Jarrabawar shiga Jami’a ta kara kaimi wajen dakile irin wadannan matsaloli. Saboda bai dace dalibai suna bayyana sakamakon jarrabawa daban da wanda yake a hannun Hukumar ba.”
“Saboda ko shakka babu wannan abin takaici ne kuma kalubale ne ga harkokin ilimi, musamman jami’o’i da sauran manyan makarantu wadanda irin wannan kasassaba zai shafa.”
Dr. Habibu ya kara da cewa, ba za a zargi Hukumar Tsara Jarabawar shiga Jami’a ba kai-tsaye, saboda ita ce ta bankado almundahanar makin da suka ce sun samu, sabanin yadda yake a ka’ida; ita Hukumar ce ya dace ta fadi sakamakon, ba dalibi da kansa ba.
“Sannan ina ga ya dace a ce manyan makarantu da kungiyoyi su rinka gudanar da bincike kan haka, kafin su ba su kyautuka ko karramawa da makamantansu. Saboda irin haka ne ya jawo abin da ya faru na aringizon makin da wata daliba ta yi a jihar Anambara.”
“Har ila yau, akwai wani hanzari ba gudu ba, wasu iyaye na nuna ci-da-zucin (idonsu a rufe) burin su shi ne ya za a yi `ya’yansu su samu maki mai yawa da samun sakamakon jarrabawa mai kyau, amma ba ilimi ba. Wannan yana daga cikin kalubalen da harkokin ilimi ke fuskanta a Nijeriya.” In ji shi
Shima a nashi ra’ayin, Dr. Auwalu Rabi’u, na Tsangayar Ilimin Kimiyya a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya ce wadannan su ne kalubalen da suke fuskanta a jami’o’in kasar nan, musamman sai ka ga dalibi ya fado Jami’a ba tare da ingantacciyar shimfidar da ya dace ya samu ba.
“Yanzu haka ina makin jarrabawar dalibai, abin mamaki sai ka tarar dalibi ko lambarsa bai iya rubutawa daidai ba, ballantana ya rubuta abin da ya dace. Sannan wannan shi ne `yar manuniya dangane da abubuwan da suke gudana a kasa baki daya a fannin karatun jami’a da manyan makarantu.”
“Lura da halin da ake ciki yanzu, hakan yana bayyana yadda rashin gaskiya ke neman ya yi katutu a zukatan jama’a, kuma hakan bai rasa nasaba da yadda aka tsuke hanyoyin shiga jami’o’in kasar nan, wanda kusan kowa yake neman ko ta halin-kaka ya samu ya shiga.”
Malam Auwalu ya bayar da shawarar cewa, “Ya zama wajibi ga kowane bangaren al’ummar kasar nan ya tashi tsaye a hada hannu a yaki wadannan matsalolin, sannan a kara kaimi wajen daukar matakan dakile aukuwar hakan. Saboda yana yiwuwa an rubuta jarrabawar cikin tsanaki amma a samu matsala wajen fitar da sakamakon.” In ji shi.