Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) Reshen Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin rassa biyu a Ɓilliri da Dukku da kuma samar da sabbin motocin sintiri biyu ga waɗannan rassa biyu da Gwamnatin Tarayya ta samar don inganta ayyukan hukumar.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da ofisishin, Kwamandan Hukumar na Jihar, Felix Theman, ya ce hakan zai taimaka matuƙa wajen rage haddura a hanyoyi da kuma tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
- Sallah: Yadda Sarkin Gombe Ya Jagoranci Hawan Daba
- Daminar Bana: Gwamnan Gombe Ya Kaddamar Da Sayar Da Taki Mai Rahusa
Theman ya ce, baya ga sabin rassan biyu, rundunar ta samar da wani ofishin a Kaltungo, yana mai albishir da cewa akwai ma ƙarin wassu huɗu da ake shirin ƙarawa.
“Hukumar FRSC reshen Jihar Gombe ta gabatar da ƙudurin ɗaga darajar wassu ofisoshinta guda huɗu da ke Ɓilliri, da Kumo, da Dukku, da Talase da Dadin-kowa da kuma cibiyoyin bincike da ake ƙira Zebra Points guda biyu a mahaɗar Kashere da Bambam.
Ganin cewa wannar buƙata na iya ɗaukar wani ɗan lokaci kafin amincewa da ita, muna buƙatar gudunmawar al’ummomin waɗannan yankuna don ba mu damar cimma muradun mu. Don haka a ƙoƙarin da muke yi ya dace da manufarmu ta yin sintiri akan hanyoyi don aiwatar da ayyukanmu yadda ya kamata, da kuma kai ɗaukin gaggawa idan buƙatar hakan ta taso kamar yadda dokokin aikinmu suka tanadar”.
Kwamandan ya nemi goyon baya da haɗin kan masu ruwa da tsaki musamman masu amfani da hanyoyi wajen tabbatar da tsaro da kare lafiya a kan hanyoyin jihar, yana mai cewa cimma hakan wani nauyi ne daya rataya a wuyan kowa.