Gwamnan Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya kaddamar da sayar da takin zamani na daminar bana da nufin bunkasa noma a jihar.
Da yake kaddamar da takin a gidan gona na Lawanti da ke karamar hukumar Akko, gwamnan ya ce za a sayar da takin ne kan kudi Naira 19,000 kan kowane buhu, sabanin farashin kasuwa da ya kai kusan Naira 26,000, don samarwa manoman jihar sauki.
- EFCC Ta Sallami Ortom Bayan Tsare Shi Na Tsawon Sa’o’i
- Gamayyar Masu Ruwa Da Tsaki A Harkar Ilimi Sun Goyi Bayan Gwamnatin Kano Na Kwato Filayen Makarantu
Gwamnan ya ce, “Gwamnati ta sayo tirela 160 na takin kan kudi Naira biliyan biyu da miliyan dari takwas da talatin, karin kimanin tireloli 35 kenan a kan na bara.”
Don tabbatar da cewa takin ya kai ga ainihin manoma, Gwamna Inuwa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da ingantaccen tsarin sayar da shi a dukkan gundumomin jihar 114 don tabbatar da cewa takin ya kai ga manoma na hakika tun daga tushe.
“Mun fahimci cewa tsadar taki da sauran kayayyakin amfanin gona na iya zama babban cikas ga manomanmu, don haka ne muke aiki tukuru wajen samar da wannan taki a farashi mai rahusa don ragewa manomanmu dawainiyar kudi.
“Burinmu shi ne mu tallafa musu da muhimman kayan aikin noma don bunkasa amfanin gona da inganta kasa, da habaka ribar da suke samu, da kuma tabbatar da dorewar harkokin noma a jiharmu”.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka da shirye-shirye daban-daban na inganta harkar noma a Gombe, don haka jihar ta shiga cikin harkoki da tsare-tsaren noma da dama a matakin jiha da shiyya da kuma kasa baki daya don bunkasa harkar ta noma.
“Gwamnati ta kuma samar da shirin tallafi na ‘NG-cares’ don samar da taki da sinadaran noma ga manomanmu kyauta, mun kuma hada gwiwa da ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya wajen horar da manoma kan noman masara da doya, inda aka bai wa wadanda suka amfana kayan aikin da suka dace don nomansu.”
Sai ya yi kira ga manoman su bai wa wadanda aka dorawa alhakin sayar da takin da rarraba shi a fadin jihar hadin kai don samun nasarar aikin.
Ya kuma gargade su, da su guji karkatar da takin.
Ya kara da cewa Jihar Gombe jiha ce ta noma, inda fiye da kaso 80 cikin dari na al’ummarta manoma ne, “Saboda haka tallafawa wannan bangare yana da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki, da samar da abinci, da dorewar rayuwar jama’armu”.
Tun farko a jawabinsa na maraba, Daraktan Tsare-Tsare, Bincike da Kididdiga a Ma’aikatar Noma da Kiwo, Dakta Ibrahim Yakubu Usman, ya ce, an kafa kwamitocin yaki da rikicin makiyaya da manoma don magance rikice-rikice da allurar rigakafin cututtukan dabbobi masu yaduwa.