Da mutum zai ce an shiga yanayi na marka-markar rusau, ruguzau da rugurguzau a jihohin Kano da Kaduna ba za a musa masa ba. Duba da irin azamar da mabanbantan shugabannin jihohin suka yi, a yunkurinsu na zuwa da sabuwar alkiblar fasalin zubin tsarin jihohin nasu. Sai dai, akwai wasu bambance-bambancen da ba a rasa ba, tattare da lamarin ruguzau ko rusau din da ke wakana a tsakanin mabanbantan jihohin biyu, Kano da Kaduna. Cikin wannan rubutu, alkalamin zai nufi Jihar Kano ne farko, sai daga bisani ne zai waiwayi jihar ta Kaduna da yarda Allah.
Game da lamarin rusau a Kano da sabuwar gwamnatin NNPP ke yi, a karkashin jagorancin mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), inda matsalar take shi ne, shin, ta wace mahanga ce mutumin Kano da waninsa a yau, ke kallo, ko fassara lamarin?. Ko da yake yanzu an tafi hutun rabin lokaci a Kotu, kafin gwamnatin ta zo ta dora daga inda ta tsaya.
- Sin Da Amurka Na Da Bukatar Karfafa Hadin Gwiwa, In Ji Firaministan Kasar Sin
- Ina Son Kara Aure, Ko Me Yake Kawo Matsaloli Tsakanin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance?
An wayigari, wani na kallon cancanta ko rashin cancantar wannan salo na ruguzau ta mahangar siyasa ne, wani ta mahangar addini ne, wani ta mahangar doka ne, sannan, wani, na yi wa harkar kallon kurulla ne ta mahangar dimukradiyya. Kallon sha’anin na ruguzau ta mahangar addini ko doka, mahanga ce mai cike fal da guna-guni tare da kace-nace maras karshe. Don me? Karkashin Kundin Dokar Zabe da kuma Kundin Tsarin Mulki na Kasa a Najeriya, haramun ne zaben kowane dantakara, faro daga kansila har zuwa kujerar shugaban kasa ta mahangar addini. Saboda haka, shigo da batun addini wajen hukunta aikin wani mai mulki a Najeriya zai zama wata sabuwar magana ce mai harshen damo! Shi ya sa da mutanen Peter Obi suka zabe shi ta mahangar addini, sai suka zamto ababen zargi a wajen ‘yan Najeriya. Shin, a nan Kano, akwai wanda ya zabi Abba Kabir, don ya yi wa mazinaci maras aure ko mashayin giya bulala?.
Idan bisa mahangar addini ce aka zabi Abba, shi ne zai ba da cikakkiyar fursar yunkurin fassara aiyukansa bisa wani mizani ko ma’auni, ko wata mahanga ta addini. Ba ka san ma cewa, ai ba zallar Musulmi ne ba kawai suka ba shi kuri’a ba. Akwai kuru’un su Diyana da Alfred cikin wadanda suka zabe shi, jeka Mazabar Sabon Gari ta karamar hukumar Fagge ka sha labari. Saboda haka, tattauna batun ruguzau din ta mahangar addini, na nufin, dole ne a saurari ra’ayin Musulmi da Kirista, tun da duk cikarsu suna da kuri’a wajen zabarsa. Sannan, ra’ayin musulmin wane bangare, da kuma kiristan wane bangare?
Haka zalika, fassara sha’anin rusau din ta mahangar Doka, shi ma dai zaune ce ba ta kare ba. Wasu na yin musu kamar haka;
Malam Abashe; “To ai doka ce ta bai wa tsohon gwamna ikon gididdiba wurare a jihar Kano”.
Malam Tanimu; “To ai wannan dokar da kake fadi, ita ce ta bai wa sabon gwamna ikon kwace duk wasu wurare da aka gididdiba kafinsa”.
Irin wadancan kalamai ne za ka ji suna tashi a kullum a Kano, wadanda ke fitowa daga bakunan lauyoyin gaske da lauyoyin sa-kai dare da rana. Hatta lauyoyin na gaske, ba duk wani abu da suke fadi ba ne Alkali ke amsa a matsayin wata hujja ko daidai. Da daman lokuta ma, Kotu na yin wurgi da abubuwan da ke fitowa daga bakunan Lauyoyin! To kuma ina ga maganganun da Lauyoyin Sa-kai ke amayarwa game da lamarin na ruguzau a Kano? Zai fi zama salama, jama’a su daina wahalar da kansu cikin batun da ke da sarkakiyar shari’a, koko hakikicewa bisa gaibun abinda mutum bai da masaniya a kansa!
Mahanga ta Siyasa da kuma mahanga ta Dimokradiyya, ba ka da wata mahanga sama da wadannan biyu, wajen yin kalubale, ko yaba wani aiki da wani mutum zababbe zai aikata, bayan samun nasarar darewa bisa kujerar iko a Najeriya. Sawa’un, kujerar da ya hau, ta Kansila ce, ko ta Danmajalisa ce, ko ta Gwamna ce, koko ta Shugaban Kasa.
Hatta kallon abu ta mahangar siyasa, sai a ga cewa, hangen namu ba ya rasa wata lam’a a tattare da shi, duba da cewa, da daman mutane ba su kai ga fahimtar hakikanin fassarar da masana ke yi wa kalmar ta Siyasa ba, kamar yadda babban malami farfesa A.A. Ujo ke fadi. Farfesan ya ci gaba da cewa, wannan munana fahimta da kuma zato da ake yi wa kalmar ta siyasa, ko kadan bai takaita ba kawai ba ga mutane da suke jahilai, saboda hatta mutane masana abin da suke riyawa ke nan. Masana irin Injiniyoyi, Likitoci da sauransu, na fassara kalmar siyasar ne a murde, in ji Farfesa: a wajensu, siyasa ba ta zamto wata aba ba, face murdiya, fuska biyu, kan-fanka, ha’inci da ma sauran wasu fassare-fassaren da ko alama ba shi ne hakikanin fassarar kalmar ba a mahanga ta ilmi.
Ma’anar Kalmar Siyasa
Kalmar Siyasa ta jima da samun tarin mabanbantan ma’anoni Kwando-kwando daga bangarorin masana kimiyyar siyasa. Sai dai kowace irin fassara da masanan za su gabatar, sai a ga tana da mahalli na kwabo da kwabo da irin yadda harkokin jama’a ko gwamnati ke gudana a cikin sha’anin rayuwarmu ta yau da kullum.
“An kalli Siyasa a matsayin wata hanya ce da gwamnati ke samar da, ko a ce kirkirar wasu manufofinta da aikace-aikaceta, tare da aiwatar da su” (Fagge & Alabi, 2007: 87-88) (Dahl, 1950: 1–5).
Mai karatu ba shi da bukatar a gwaggwafe a na kokarin ankarar da shi cewa, rusau ko ruguzau da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yi, na daga manufofin gwamnatin ne. Hakika, yin rusau din, na daga manya-manyan shirye-shiryen da gwamnatin ta taho da su cikin angararta, wanda shi ne bayan cikar muradin an zabe ta, sai take aiwatar da su dare da rana.
A ko’ina cikin Duniya, sanannen abu ne cewa, kusan kowace gwamnati akwai wani abu da za a ga a kansa ne tafi mayar da hankalinta. Mun sha ji a can kasashen Turai, a kan sami wasu jam’iyyun da suka fi mayar da hankali ne kacokan ga ma’aikata, saboda haka, idan suka sami nasarar lashe zabe, sai a ga rayuwar ma’aikata na samun wani tagomashi na musamman.
Gwamnatoci irin na Isra’ila kuwa, kabilanci da kassara raunanan Palasdinawa ne manyan abubuwan da suka sanya a gaba, bugu da kari, duk wanda bai da irin wannan tunani kuwa, babu shi babu samun tikitin takara a wajen Yahudawan na Isra’ila!. Daga wasu manufofin jam’iyyun siyasa a Turai, duk wani bakon-haure ba shi da tabbacin samun wata sawaba a Kasar. Wata gwamnatin cikin sasannin Duniya, na tsantsar nuna kyama da kuma adawa ne da duk wasu manufofi irin na ‘yan jari-hujja! Haka abubuwa ke ta tafiya a ciki da wajen Najeriya, idan a na maganar mabanbantan manufofi da gwamnati ke zuwa da shi sabanin wadda ta gabace ta.
Bambancin Manufofin NEPU Da NPC (PRP da NPN)
Ba ma sai an tafi can da nisa ba, ko a cikin wannan Kasa tamu ta Najeriya, an sami banbancin manufofi a tsakanin jam’iyyun NEPU da NPC: irin wadannan mabanbantan manufofin jam’iyyun biyu da aka yi cikin Jamhuriyar Siyasa ta farko a wannan Kasa, su ne suka sake yin geza har zuwa cikin Jamhuriyar Siyasa ta biyu, tare da sajewa cikin jam’iyyun siyasun PRP da kuma NPN. Babbancin manufofin da ke tsakanin jam’iyyun biyu ya zafafa fiye da duk inda mai karatu ke tunani. Bugu da kari, tun daga jam’iyyun na NPC da NEPU, har zuwa PRP da NPN, za a samu cewa, sun sami nasarar kafa gwamnatoci cikin wasu yankuna a Kasar. Bayan kafa gwamnatin, kowace jam’iyya cikinsu na kokarin zuwa ne da manufar da ta saba da na abokiyar adawarta.
Kawar Da Haraji Da Jangali
Cikin Jamhuriyar Siyasa ta biyu ne jam’iyyar PRP ta kawar da wasu haraji-haraji da mutanen NPC suka jima suna da karba tsawon lokaci daga jama’ar Arewacin wannan Kasa. Tamkar irin yadda a yau za a ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta hana a karbi wani haraji daga mutanen da ke da karfin jari daga naira dubu talatin (N30,000) zuwa kasa, alhali gwamnatin APC karkashin tsohon gwamna Ganduje, sun dauki tsawon Shekaru suna karbar haraji hatta daga mutumin ma da ke da jari na kasa da naira dubu goma (N10,000), je ka Kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi ta Sabon Gari ka sha labari.
Har ila yau, a fahimatar wasu, kamar yadda gwamnatin PRP a karkashin jagorancin Muhammadu Abubakar Rimi ta kafa wani kakkarfan Kwamiti, don kwato wa jama’ar Kano musamman talakawa wasu hakkokinsu da suka hada da gonaki da sauransu, da wasu manyan mutane shafaffu da mai suka yi a baya, misalin haka ne manufar Abba Gida-Gida na dawo wa da jama’ar Kano filayensu da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta sabautar da su ga masu hannu da shuni, wanda hakan ne silar yin rushe-rushen.
Kamanceceniyar Manufofin PRP da NNPP
Kamar yadda masana da masu tarin Shekaru suka sani cewa, an yi nakudar jam’iyyar PRP ne tun daga gyatumarta NEPU, da mutum zai duba sananniyar Shelar Sawaba “Sawaba Declaration” da NEPU ta yi, to a kansu ne ma manufofin jam’iyyar PRP suka tafi.
Waccan Shela, ta cika ce da kalubalantar wadanda ake gani sun yi rub da ciki bisa hakkokin raunanan mutane talakawa wadanda su ne mafiya rinjaye. Cikin Shelar, akwai cin-alwashin dawo wa da raunanan mutane ‘yancinsu da hakkunansu da manyan mutane suka yi lakur a kai, tamkar irin yadda jam’iyyar NNPP ke ta yin babatu a kai dab da zabe.
Kamar irin yadda a kullum kamfen din NNPP ke ta balokoko a kan talaka-talaka, wanda har wasu manya ke kallon cin zabenta wata barazana ce a wajensu, tamkar haka ne ma PRP take a wajen manyan kasa lokacinta.
Kamar irin yadda jam’iyyar PRP ke ta mayar da ‘ya’yan talakawa su zama mutane, wasu ma na da ra’ayin cewa, irin hakan ne babban abin da NNPP ke yi, ta hanyar fitar da ‘ya’yan talakawa zuwa kasashen waje don yin karatu mai zurfi.
Mu tara mako mai zuwa domin ci gaba.