An kammala taron duniya kan fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, jiya Asabar a birnin Shanghai na kasar Sin, inda aka samu yarjejeniyoyin ciniki da na zuba jari da darajarsu ta kai biliyoyin dalar Amurka.
Wu Jincheng, daraktan hukumar kula da tattalin arziki da fasahar sadarwa ta birnin Shanghai, ya ce an sanya hannu kan yarjejeniyoyin ciniki da darajarsu ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 11, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.5, da yarjejeniyoyin zuba jari kan wasu manyan ayyuka 32 da darajarsu ta kai yuan biliyan 28.8.
Sama da kamfanoni 400 ne suka halarci taron na bana, da aka yi a wuri mai fadin murabba’in mita 50,000. Kuma wadannan adadi su ne mafi koli da aka samu tun bayan na shekarar 2018 da aka kaddamar da taron a karon farko.
Haka kuma yayin taron, an gabatar da wasu sabbin kayayyaki guda 30.
A cewar Wu Jincheng, Shanghai za ta yi cikakken amfani da kyakkyawan tasirin taron wajen inganta raya masana’antar fasahar AI cikin aminci. (Fa’iza)