Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya zama sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS.
An cimma wannan matsayar ne a yayin taron kungiyar na shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar tattalin arzikin kasa karo na 63 a birnin Bissau, babban birnin Guinea-Bissau a ranar Lahadi.
- Tinubu Ya Isa Guinea-Bissau Domin Taron ECOWAS, Ya Ziyarci Sojojin Nijeriya
- Gobe Tinubu Zai Tafi Guinea-Bissau Halartar Taron ECOWAS
A matsayinsa na shugaban kungiyar, Tinubu zai taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar kasashe mambobin ECOWAS wajen bunkasa tattalin arziki, daidaiton siyasa, da hadin kai.
A matsayinsa na sabon shugaban da aka nada, Tinubu zai hada kai da kasashe mambobin kungiyar, cibiyoyin yanki, da abokan huldar kasa da kasa don aiwatar da tsare-tsare na bunkasa tattalin arziki, hada-hadar kasuwanci a yankin, da ci gaban zamantakewa.
Kazalika, ana sa ran zai mayar da hankali wajen karfafa hadin guiwar ECOWAS game da barazanar tsaro da samar da hadin guiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar wajen tunkarar kalubalen yankin.