Kungiyar likitoci a Jihar jihar Nasarawa, ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar, inda ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin mako biyu da ta biya musu dukkan bukatunsu.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne bayan gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da karin matsayi ga wasu mambobin kungiyar har na tsawon shekaru tara da karin albashi sama da shekaru 12.
- Bidiyon Dala: Kungiya Ta Bukaci A Hana Ganduje Tserewa Daga NijeriyaÂ
- Ban Bada Umarnin Rufe Majami’ar Fadar Shugaban Kasa Ba —Remi Tinubu
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron gaggawa na majalisar da ta gudanar a Lafia babban birnin jihar, shugaban kungiyar a jihar, Dakta Peter Attah, ya bayyana cewa sun yanke shawarar dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar ne domin rage wahalhalun da al’ummar jihar suka shiga.
Attah, ya ce kungiyar ta umarci mambobinta da su koma bakin aiki cikin gaggawa domin ceton rayuka.
Idan za a iya tunawa, tun a ranar 13 ga watan Yunin 2023 ne, kungiyar ta ba da wa’adin kwanaki 21 don biya mata bukata kafin ta shiga yajin aikin na gargadi.