Kungiyar Masu Gidajen Burodi burodi, ta yanke hukuncin kara farashin kudin burodi da kashi 15 cikin dari daga ranar 24 ga watan Yuli, 2023.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan kammala taron shugabanninta na kasa, kungiyar ta ‘Association of Master Bakers and Caterers of Nigeria’ ta ce ta dauki matakin ne bayan la’akari da hauhawar farashin kayan masarufi.
- Yau Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Emefiele Ya Shigar
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Neja Ta Umarci Masu Gidaje A Hanyoyin Ruwa Su Tashi
“An umarci dukkanin shugabannin kungiyar na yanki su tabbatar cewa ‘ya’yan kungiyar sun bi wannan umarni, har sai idan sun samu wani sabon umarnin daga uwar kungiyar ta kasa.”
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Mansur Umar, ta ce tashin farashin ya biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
A ranar 29 ga watan Mayu 2023 ne, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a cikin jawabinsa na karbar mulki.
Lamarin ya haifar da tashin litar man fetur daga kimanin naira 200 zuwa sama da naira 500.
Kungiyar ta ce abubuwan da ta ke amfani da su wajen gudanar da sana’ar burodi, wadanda suka hada da man fetur da gas da fulawa da suga da sauransu duk sun yi tashin gwauron zabi.
Kazalika, kungiyar ta koka kan yadda hukumomi a kasar nan karbar haraji masu yawan gaske.
A baya dai an sha kai ruwa rana da kungiyar kan karin farashin burodi.
A yanzu haka dai burodi ya fi karfin sayen mai karamin karfi, inda a wasu yankunan masu gidajen suka rufe saboda tsanantsr tsadar kayan aiki.