Gwamnatin Jihar Neja ta ba da umurnin kawo karshen matsalar tsaro tare da tabbatar an zakulo duk masu hannu a ciki, domib kawo karshen matsalar a jihar.
Gwamnan Neja, Rt. Hon. Muhammad.Umar Bago ne ya ba da umurnin a lokacin da ya kai wa mai martaba sarkin Minna, Dakta Umar Faruk Bahago ziyarar sallah a fadarsa a yunkurinsa na ziyartar masarautun jihar.
- Kotu Ta Umarci DSS Ta Saki Emefiele Cikin Mako Daya
- ‘Yan Majalisar Dokokin Nijeriya Sun Bukaci Karin Albashi
Gwamnan ya jajanta wa sarkin bisa harin da wasu ‘yan fashi suka kai wa mai biyan kudin fadar sarkin, ya tabbatar wa sarkin cewar gwamnatinsa za ta tabbatar ta samar da ingantaccen tsaro domin tsare rayuka da dukiyar jama’a.
A cewar gwamnan, “Muna kan lalubo hanyar magance matsalar, kuma za mu tabbatar wannan abin ya zama tarihi. Saboda haka mun ba da umurnin ganin an tsayar da wannan abin tare da tabbatar an kamo masu hannu a wannan lamarin a Mina da sauran sassan jihar.
“Ba zan lamunci fadan matasa ba (‘yan daba) a jihar ba, na gargadi jami’an hukumar shari’a da su guji ba da belin wadanda ake tuhuma ba bisa ka’ida ba ko yin yafiya ga ‘yan ta’adda.”
Gwamnan ya ce makarantun da aka rufe saboda matsalar tsaro za a bude su kuma ‘yan gudun hijira za su koma gidajensu cikin kwanciyar hankali. Ya ce akwai bukatar manoma su mayar da hankali kan gonakinsu. Ya kara da cewar takin zamani zai samu cikin saukin farashi wanda za a kaddamar da shi a wannan makon.