“Na mu ya samu”, wannan ita ce kalmar da sabon shugaban Gidan Radio Kano, MD Hisham Habib, ya fara furtawa a cikin raha a lokacin da wakilinmu ya buga masa waya domin yin addu’ar Allah ya taya ruko, bayan sanarwa daga mukaddashin daraktan yada labarai na gwamnan Kano ya ba da sanarwar nada shi wannan mukami.
Hisham ya kasance tsaohon wakilin LEADERSHIP a Kano, inda ya yanzu ya zama sabon shugaban Gidan Rediyo Kano a wannan makon da ya gabata a wannan lokaci. Gidan Rediyo Kano wanda ya haura shekarau 70 da kafuwa yana da take ko lakabi na ‘uwa ba da mama ga ‘ya’yanta’.
- Abin Da Ya Sa ‘Yan Nijeriya Ba Su Mori Dimokuradiyya Ba Har Yanzu –Jega
- Musabbabin Haramta Sana’ar Gwangwan A Jihar Borno
Shi dai Hisham, ya kasance gogaggen dan jarida wanda ya yi aiki a karkashin gwamnantin Jihar Kano da sauran manyan gidajan jaridu na arewa da na kudanci, wanda hakan ta ba shi dammar zama kwararan dan jarida mai zaman kansa, kuma ya kasance shugaba na kamfani yada labarai na ‘NEWS TUNNE’, mai yada labaransa ta Internet, wannan ce ta sa wasu ke kiransa ko kallasa a matsayin wanda ya san aikin jarida na zamani da kuma na da.
Yanzu haka dai ‘yan’uwa da abokan aiki na ta tururuwar ziyararsa na masa addu’ar fatan alkairi na samon kyakkyawan jagoranci daga sabon shugaban gidan rediyo na Kano, wanda tuni ya shiga ofis domin kama aiki gadan-gadan.