Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya halarci bikin mika tashar jirgin saman kasa da kasa ta Mugabe da aka gudanar ranar Jumma’ar da ta gabata, inda ya bayyana cewa, tallafin da kasar Sin ta bayar don ayyukan samar da ababan more rayuwar jama’ar kasar Zimbabwe a fannonin makamashi, da sufuri, da kiwon lafiya ya nuna dangantakar abokantaka ta dogon lokaci a tsakanin kasashen biyu.
A watan Yunin wannan shekara ne, aka kammala aikin gina tashar jirgin saman Mugabe. A jawabin da shugaba Mnangagwa ya yi bayan ya ziyarci ginin tashar a wannan rana, ya ce kayayyakin zamani na tashar jirgin sun kai matsayin kasa da kasa, kuma ya yaba da ingancin aikin kamfanin kasar Sin da ya yi aikin gina tashar jiragen sama ta kasa da kasa.
Mnangagwa ya ce, gina filin tashi da saukar jiragen sama na Mugabe, ya haifar da bunkasar tattalin arzikin cikin gida, ya kuma kawo sabbin fasahohi, da samar da guraben ayyukan yi. Ya kuma nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin bisa goyon bayan da ta dade tana baiwa kasar Zimbabwe.
Rahotanni na cewa, an kadamar da aikin gyara da fadada filin jirgin saman Mugabe ne a shekarar 2018. Bayan kammala aikin, ana sa ran yawan fasinjojin da ke tashi da sauka ta filin jirgin, zai karu daga mutane miliyan 2.5 a kowace shekara zuwa mutane miliyan 6. (Mai fassara: Ibrahim)