Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara bin diddigin Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, kan gazawarsa wajen bayyana inda kudade sama da Naira biliyan 32 da jam’iyyar ta tara daga sayar da fom din takara a zaben 2023.
Wata majiya a hukumar EFCC ta tabbatarwa da WHISTLER cewa, jami’an EFCC sun ziyarci gidan Abdullahi Adamu a ranar Lahadin da ta gabata da daddare bayan da aka rahoto cewa, ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
Jami’an EFCC sun ziyarci gidansa da ke kan Ali Akilu Crescent, da ke fadar Aso Rock Villa tare da takardar izinin bincike da misalin karfe 8 na dare.
Jami’in EFCC da ya shaida wannan rahoto kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce, shi ba ya cikin tawagar da ta je gidan shugaban, amma wani abokin aikinsa da ke cikin tawagar ya shaida masa cewa, jami’an ‘yansanda da ke gadin gidan Adamu sun hana su shiga gidan.
Har zuwa lokacin buga wannan rahoto, Kakakin hukumar EFCC bai amsa kira da sakonnin da aka aika masa ba domin jin ta bakinsa.