Marcus Rashford ya sanya hannu kan sabon kwantiragin shekaru biyar da Manchester United.
Sabon kwantiragin Rashford zai sa ya rika karbar fam 300,000 duk mako, wanda zai ba shi fam miliyan 78 a shekara.
- Lauyoyi 60 Sun Yi Karar DSS Kan Kin Sakin Emefiele
- Ƙasa Da Sa’o’i 24 Da Sauka: EFCC Ta Ziyarci Tsohon Shugaban APC Abdullahi Adamu
Sabon kwantiragin na nufin Rashford zai kasance daya daga cikin ‘yan wasan Ingila mafi yawan albashi.
Marcus Rashford zai rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta shekaru biyar akan kudi fam miliyan 78 a Manchester United.
Rashford ya amince da kwantiragin fam 300,000 a duk mako wanda zai ci gaba har zuwa 2028 kuma ana shirin sanya hannu a wannan makon.
Dan wasan mai shekaru 25 ya shiga watanni 12 na karshe na kwantiraginsa da ake biyansa fam 250,000 a duk mako.
Karin albashin fam 50,000 duk mako na nufin Rashford zai ci gaba da zama a matsayin daya daga cikin yan wasan Ingila da ke karbar albashi mafi tsoka.
Raheem Sterling na Chelsea ne kawai aka yi imanin yana samun irin wannan albashi.
Dan kasar Ingilar ya wanda ya jefa kwallaye 30 a kakar 2021-22 ya zama dan wasan United na farko tun bayan Robin van Persie shekaru goma da suka wuce da ya ci wa kulob din kwallaye 30.
Rashford dai ya fara atisayen tunkarar kakar wasa tare da sauran ‘yan wasan United na kasa da kasa ranar Lahadi.
Don haka ba zai shiga wasan sada zumunta da za su yi da Lyon a daren Laraba a Murrayfield ba, bayan da bai samu buga karawarsu da Leeds a Oslo a makon jiya ba.