Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad Abdulkadir ya rushe dukkanin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar nan take.Â
Hakan ya biyo bayan karewar wa’adin mulkinsu ne a matsayin shugabannin rikon kwarya.
- Da Dumi-Dumi: Farashin Man Fetur Ya Tashi Zuwa 617 Kan Kowace Lita
- Dajarar Naira Ta Sake Faduwa Zuwa 803 Akan Kowace Dalar Amurka
Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim ne, ya bayyana amincewar gwamnan cikin wata sanarwar da ya raba wa ‘yan jarida a Bauchi a ranar Talata.
A cewar sanarwar, an umarci dukkanin shugabannin da su mika ragamar tafiyar da harkokin kananan hukumominsu ga manyan jami’an sashen gudanar da mulki na kananan hukumomin har zuwa lokacin da za a nada wasu.
Bala Muhammad, ya yi fatan alkairi ga mambobin kwamitin rikon kwarya na kananan hukumomi masu barin gado tare da musu fatan samu nasarori a rayuwarsu ta gaba.
Ya kuma ya ba musu kan gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban kananan hukumomin nasu.