Tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura, ya kawo karshen yamadidin da ake ta yadawa da cewa akwai rashin jituwa da rikici a tsakaninsa da magajinsa wato Gwamna Abdullahi Sule.
Al-Makura, wanda kuma tsohon Sanata ne da ya wakilci mazabar Nasarawa ta kudu a majalisar dattawa, ya misalta batun da cewa kwanzon kurege ne.
Sanata Al-Makura ya shugabanci jihar Nasarawa ne tun daga shekarar 2011 kana ya mika mulki ga Sule a ranar 29 ga watan Mayun 2019.
Ya ce, masu yada batun barakar, kawai wasu marasa kishi ne da karfi da yaji suke son hada fitina a tsakinsa da magajinsa Gwamna Sule.
Ya warware batun ne a lokacin da ke gamawa da ‘yan jarida a wata ziyarar kashin kai da ya kai wa Gwamna Sule a gidan gwamnatin Nasarawa da ke Abuja a ranar Laraba.
Ya ce: “Jita-jita shi ne man da ke kara rura siyasa. Idan babu jita-jita da tsegumi, zai zama ba mu buga siyasa ke nan.
“Akwai wasu mutanen da sun kware a kimtsa rudani a siyasance, da kuma gutsuri-tsomen suke neman gindin zama a jikin masu mulki.”
Tsohon Gwamnan ta ce shi da Gwamna sun fahimci kansu kuma suna tafiyar da siyasarsu ta yadda ba za su bai wa masu kokarin farraka tsakaninsu dama ba, ya kara da cewa ta hanyar yin aiki a tsakaninsu tare za su bada gudunmawar su wajen cigaban jihar Nasarawa.
Ya kuma yaba da salon mulkin Gwamna Sule tare da cewa jihar ta samu ayyukan bunkasa a karkashin gwamnati mai ci.