Wasu daga cikin ‘yan majalisar jihar Zamfara sun ce babu wani dalili da zai sa gwamnatin jihar ta yi sulhu da ‘yan fashi a jihar.
Honarabul Hamisu A Faru, mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta Kudu a majalisar dokokin jihar ne, ya bayyana hakan cikin hirarsa da BBC Hausa.
- Ganduje Na Iya Maye Gurbin Adamu A Matsayin Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa
- A Karon Farko Bayan Barin Mulki, Buhari Ya Halarci Taro A Katsina
Ya ce “Babu yadda za a yi sulhu da mutumin da bai san Allah ba”.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan da ‘yan fashin daji suka kori mazauna wani kauye gaba dayansu a cikin daya daga kananan hukumomin da yake wakilta kana suka mayar da shi sansaninsu.
Dan Majalisar ya ce “Gwamnan jihar ya fito ya kalubalanci duk wani mai neman a yi sulhu da ‘yan fashin” wanda hakan ne ya kara musu karfin gwiwa a wannan tafiya.
Ya ce akwai firgici a halin da ake ciki a jihar yanzu, domin barayin sun tsallaka titin Gurusu sun bi Barayar zaki sun tsallaka Gulbi sun je wani kauyen Rafin Gero da ake ce masa Gyado sun yi sansani, yau tsawon kwana 10 kenan.
Ya kara da cewa kalubalen da ake fuskanta a yanzu shi ne an shiga damuna, lokacin da yaki da wadannan bata-gari ke da wuya.
“Da yawan dazuka itatuwansu sun yi kore sun zama duhuwa, tsakaninka da mutane ba tazara mai yawa amma duhu ba zai barku kuga juna ba.
“Shekaran jiya sun shiga kauyukan Ruwan rana da Yashi sun kone shaguna da kuma dukiya mai yawa,” in ji Hamisu A Faru.
‘Yan fashin daji sun dauki tsawon shekaru suna kai hare-hare a jihar Zamfara da ma jihohin da suka yi makwabtaka da ita irin su; Katsina, Sakkwato da Kaduna.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da sanya da dama zama ‘yan gudun hijira.
Sai dai wasu na ganin yin sulhu da ‘yan fashin dajin na iya kawo sauki ga hare-haren nasu, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar kin amsar wannan shawara.