Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce jarin waje da kamfanonin Sin suka zuba kai tsaye a kasashen waje, ya karu a watanni shida na farkon shekarar bana.
Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Alhamis din nan, sun nuna cewa adadin darajar jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje a fannonin da ba na tsabar kudi ba, ya karu da kaso 22.7 bisa dari, inda ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 431.61, a rabin farko na shekarar ta 2023.
Kaza lika a dalar Amurka, adadin darajar jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje a dukkan fannoni wato ODI a Turance ya kai biliyan 62.29, adadin da ya kadu da kaso 14.8 bisa dari, idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata. (Saminu Alhassan)