Ana ci gaba da cece-kuce a kan yadda za a raba Naira Biliyan 500 da gwamnatin Tinubu ta ware don rage radadin talauci da aka shiga sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.
Bagarorin al’umma da dama sun nuna rashin dacewar raba kudin suna masu cewa, kamata ya yi a zuba kudin a wasu bangarorin tattalin arzikin kasa da zai samar wa al’umma Nijeriya sauki, wasu kuma na ganin alfanun rarraba kudin suna masu cewa, in har aka raba kudin yadda ya kamata ba tare da nuna banbanci ba, to lallai al’umma da dama za su amfana kuma zai rage musu halin kunci da aka shiga, musamman ganin yadda ake fuskantar hauhawar farashin kayan abinci da aka dade ba a taba gani ba a ‘yan shekarun nan.
Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar raba wa magidanta ‘yan Nijeriya miliyan 12 naira dubu takwas kowanne su don rage radadin talauci sakamakon cire tallafin man fetur da ta yi a ranar 29 ga watan Mayu, daidai lokacin da aka rantsar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Majalisar kasa ta amince da Naira Biliyan 819.5 a matsayin kasafin kudi na gaggawa kashi na biyu, na shekarar 2023 don ganin an ware wa dukkan bangarori kudaden da suke kamata na kammala ayyukan da ke a gaba wanda gwamnatin Buhari ta fara, har zuwa lokacin da za a gabatar da cikakken kasafin kudi na shekara gaba daya kamar yadda aka saba. A cikin kasafin kudin an ware Naira Biliyan 500 don samar da tallafi saboda radadin da al’ummar Nijeriya suka shiga sakamakon cire tallafin man. Byanin yadda za kashe kasafin kudin ya nuna cewa sabbin ‘yan majalisa 469 za su raba Naira biliyan 70 wajen farfado da rayuwarsu ta yadda za su iya fuskantar ayyukan majalisa. Sai dai mutane da sun koka a kan yadda ba a sanya ma’aikata da sauran ‘yan Nijeriya cikin wannan garabasar ba tare da bayyana cewa an yi rashin adalci.
Tabbatar da cikakken adalci a harkar samar da ci gaban tattalin arziki a kasa yana da matukar muhimmanci, a kan haka ne aka samo tsarin raba kudaden da zai yi wa dukkan bangarorin kasa adalci wajen ba kowacce jiha kudin da ya kamata. Matukar an yi rabon cikin adalci, gwamnatocin jihohi za su samu kwarin gwiwar gudanar da mulkinsu cikin adalci ta yadda dukkan masu ruwa da tsaki za su amfana.
Gwamnati ta sanar da cewa, za ta tallafa wa talakawa marasa karfi da Naira 8,000 ga kowanne magidanci da ya samu shiga shirin na tsawon wata shida inda mutum miliyan 12 za su amfana. Akalla ana sa ran mutum miliyan 64,88 daga cikin matalauta miliyan 132.93 su amfana. Wannan na nufin an bar ragowar mutum miliyan 68.05 a tutar babu.
Da ace majalisar tarayya ta amince ne kawai da Naira biliyan 500 na tallafin ba tare da ta sanya kudaden da za a kashe wajen sarrafa kudaden ba, da sai dai kawai gwamnati ta zabi mutum miliyan 10.42 wadanda za su amfana daga kudin tallafin ta yadda za a ba mutum miliyan 5.68 tallafin daga Arewacin Nijeriya yayin da mutum miliyan 4.74 za su amfana daga Kudancin Nijeriya, wannan tsarin zai kai ga ba mutum miliyan 56.32 tallafi a cikin matalautan Nijeriya, wanda haka zai kuma kai ga fitar da karin mutum miliyan 9 daga samun tallafin, a kan haka dole a gode wa majalisar kasa a kan wannan hagen nesan da ta yi a wannan bangaren.
A kiyasin da aka yi na wadanda ya kamata su amfana da wannan tallafin daga cikin matalauta a fadin tarayyar kasar nan. Akwai wadanda suka shiga cikin da’irar matalauta a Nijeriya da suka kai mutum miliyan 24.67, ya zama mutum miliyan 13.3 a arewa mutum miliyan 11.3 a yankin kudancin kasar nan, ke nan gwamnati za ta zabi mutum miliyan 12 daga cikin bangarorin gaba daya wadanda za su amfana da tallafin na naira 8,000 na tsawon wata 6 gaba daya.
A tunanin farko, Naira 8,000 a duk rana kudin zai kama Naira 267 a kullum, amma in an samu banbancin yawan iyali ga magidanci lamarin zai iya canzawa.
A yadda ake a akalla mutum 6.7 a kowanne gida a yankin arewa maso gabas, in aka basu Naira 8,000 don su yi amfani da shi a kowanne wata kowanensu zai samu Naira 1,200, Naira 40 kenan a duk rana, haka abin yake ga mutane da suke yankin Arewa ta Gabas, wadanda suke zaune a yankin arewa ta tsakiya kuma da ake da akalla mutum 5.8 za su samu naira 1,410, kowanne mutum zai samu Naira 47 ke nan a duk rana.
Wadannan alkaluman sun bambanta a yankin kudancin Nijeriya, a kudu maso yammaci inda mutum 3.8 za su raba naira 8,000, hakan zai sa su samu akalla Naira 2,088 kowanne mutum ya kama Naira 70 a duk rana. Haka kuma a yankin kudu maso gabashin Nijeriya inda mutum 4.5 za su raba Naira 8,000 na tallafin kowa zai samu Naira N1,770, ya kama naira 59 kenan a kowace rana.
Kamar yadda wata kididdiga da Daily Trust ta wallafa ta nuna, Jihohi biyar da ake sa ran za su samu kaso mafi tsoka na tallafi a Nijeriya sun hada da Kano, Kaduna, Legas, Akwa Ibom da Katsina, wannan kuma na faruwa ne saboda yawan gidajen da za su amfana da wannan tallafi na radadin man fetur. Kididdiga ta nuna za su samu Naira biliyan N5, 4.4, N4.1, N3.9, da N3.4 kowannen su. Abuja, Abia, Edo, Ondo, da Jihar Borno ne jihohi 5 da za su karbi kaso mafi karanci na tallafin man fetur da gwamanatin Tinubu za ta bayar ga talakawan Nijeriya. Hakan na faruwa ne saboda karancin gidaje masu fama da talauci a fadin jihar, a kan haka za su karbi Naira biliyan N888, N912, N1.05, N1.13, da N1.5 kowannensu.
A cikin tsarin bayar da kudin da za a dauki wata 6 ana yi, jihohin Kano, Kaduna, Legas, Adamawa, Zamfara, Nasarawa da Abiya za su karbi naira biliyan N30.3, N26, N24.4, N12.9, N10.2, N5.5 da N4.2 kowannensu.
Yankunan siyasarar kasar nan da za su karbi kaso mafi tsoka su ne, arewa maso yamma da zai samu Naira biliyan N22.9 duk wata, a wata shida kuma jimillar za ta zama naira biliyan 137.7. Yankin kudu maso kudu da kudu maso yammancin kasar nan za su karbi Naira biliyan N15.6 da naira biliyan N14.3 duk wata, a cikin wata shida kuma za su karbi Naira biliyan 93.8 da naira biliyan 85.8. Yankin kudu maso kudu ne zai samu kaso mafi karanci saboda shi ne ba shi da magidanta matalauta da yawa.
Matsalolin da za a iya fuskanta wajen rarraba wannan tallafin shi ne zimmar da ake da ita ta tabbatar da dukkan wadanda suka cancanci samun tallafin sun samu a hannunsu, sai kuma yawanci wadanda suka cancanta da ba su da asusun ajiya na banki a fadin kasar nan, lallai wannan ba karamar matsala ba ce.
Ya kamata a samar da tsari mai inganci da zai samu karbuwa ga al’umma bangarorin kasar nan.
…Za A Sake Wa Tsarin Shirin Fasali – Gwamnati
Biyo bayan ce-ce-ku-ce da jama’a ke ta famar yi, gwamnatin Tinubu ta umurci sake nazarin shirin bayar da tallafin kudi na Naira 8,000 da nufin samar da agaji ga magidanta masu karamin karfi don rage radadin cire tallafin man fetur.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya ce, gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar fifita bukatar ‘yan Nijeriya da jin dadinsu da tsaronsu fiye da bukatarta a karkashin shirin “Sabunta kwarin guiwa”, hakan ya sanya daukar matakin gaggawa.
Idan dai za a iya tunawa, bayan yanke shawarar dakatar da tallafin man fetur, gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin aiwatar da wani shiri na bayar da agaji, wanda za a dinga bayar da tallafin Naira 8,000 duk wata na tsawon watanni shida ga magidanta masu karamin karfi miliyan 12.
Sai dai shirin ya gamu da cece-kuce da suka, inda da dama ke nuna rashin jin dadi da kuma shakku kan tasiri da ingancin shirin.
Shugaba Tinubu ya ji ra’ayoyin jama’a kuma take ya umarci a yi aiki don gyara kurakuran da jama’a suka hango cikin gaggawa.