A watan Maris na 2021, zauren majalisar dinkin duniya ya ayyana 2023 a matsayin ranar bikin Gero ta duniya bisa shawarar da gwamnatin kasar Indiya ta bayar.
Sama da kasashe 70 ciki har da Nijeriya ne suka goyi bayan wannan shirin.
Nan da shekarar 2025, kafar internet da ke bibiyar farashin Gero ta ayyyana cewa, farashin Gero a kasuwar duniya, zai sama da dala biliyan 12, inda Nijeriya Indiya suka kasancesun kai kashi 80 wajen noma Gero.
A ‘yan kwanukan da suka wuce, masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma ciki har da ofishin jakancin Indiya da ke a Nijeriya da hukumar aikin gona da ke a majalisar dinkin duniya da kuma shirin samar da abinci na duniya, sun gudanar da taro a Abuja, musamman domin yin dubi akan yadda za a kara amfana da tattalin arzikin da ake samu a fannin noman Gero.
Ma’aikatar aikin gona da raya karkara ce ta sa ido akan gudanar da taron, inda mahalarta taron, suka jaddada mahimancin cewa, a fannin noman Gero, ana samun dimbin kudaden shiga da kuma samar da abinci ga ‘yan Nijeriya.
Babban sakatatre a ma’aikatar ta aikin gona da raya karkara Dakta Ernest Umakhihe a jawabinsa a wajen taron ya bayyana cewa, tsohon tirihi ga Nijeriya a wajen noma Gero , mutane sama da miliyan 500 ne ke yin amfani dashi a fadin duniya, inda ya kara da cewa, Gero na yakar yunwa a cikin alumma kuma ya kasance, afnin gona mai gina jikin bil Adama.
A cewar cibiyar aikin gona ta ICRISAT, sama da mutane miliyan 90 a yankin Asiya da nahiyar Afirka ne suke dogaro da Gero, inda kuma mutane sama da miliyan 500, a kasashe 30 suke dogaro akan Gero.
Dakta Ernest ya bayyana cewa, baya ga yin amfani da Gero a matsayin abincin da mutane ke ci, hatta dabbobi ana ba su a matsayin abinci ana kuma sarrafa shi zuwa sauran nau’uka da ban da ban ciki har da magungunan gargajiya.
Shi ma a na sa jwabin a gurin taron wakilin hukumar abinci ta duniya FAO a Nijeriya da kuma a kungiyar ECOWAS Mista Fred Kafeero ya bayyana cewa, karni da dama da suka gabata Gero ya bayar da gagarumar gudunmawa a matsayin abinci mai gina jiki a daukacin kasashen da ke a duniya, inda ya kara da cewa, Gero na jurewa kowanne yanayin da aka shuka shi.
A cewrsa, domin a kara rungumar fannin yin naomasa, akwai matukara bukatar a mayar da hankali wajen nomansa har zuwa karshen shekara da kuma kara zamanantar da yin nomansa.
Ya sanar da cewa, a bangaren hukumar za ta yin a ta kokarin wajen bayar da taimakon da ya kamata, musamman wajen nomansa ta hanyar yin amfani da kimiyyar zamani da kuma kara habaka kasuwancin sa.
Shi ma Mista Shiri G. Balasubramanjan, babban kwamishina a ofishin jakadancin Indiya a Nijeriya ya bayyana cewa, a shirin habaka noman Gero na Indiya wanda gwamnatin kasar ta kirkiro dashi bisa nufin bunkasa noman Gero da sarrafa shi da rabar dashi na ci gaba da ganin Gero ya samu karbuwa wajen yin amfani dashi a tsakanin miliyon mutane da ke a fadin duniya.
A cewarsa, gwamnatin kasar mu na habaka noman Gero musamman ganin cewa, yin amfani dashi, na karawa dan Adam kiwon lafiyarsa, inda ya kara da cewa, sama da shekaru 5000, mazuna yankin Asiya na yin amfani da Gero a matsayin abinci.
shirin habaka noman Gero na Indiya wanda gwamnatin kasar ta kirkiro dashi bisa nufin bunkasa noman Gero da sarrafa shi da rabar dashi na ci gaba da ganin Gero ya samu karbuwa wajen yin amfani dashi a tsakanin miliyon mutane da ke a fadin duniya.