Jami’an ‘yan sanda sun cafke wata mata mai suna Esther Godwin, bisa zarginta da watsa wa wata mai suna Endurance Samuel tafasasshen ruwa, wacce take zargin tana neman mijinta.
Lamarin ya afku ne a garin Idanre, yankin Karamar Hukumar Idanre.
Da take magana game da lamarin, Samuel ta musanta batun soyayya da mijin wanda ake zargin, inda ta bayyana cewa tana aiki ne a matsayin ma’aikaciya a gonar mijin na ta.
“Esther ta kira ni daga inda nake koyon sana’ar dinki don in zo na karbi kudina na man gyada da nake bin mijinta. Saboda bayan sayar da mai da nake yi ina yin wa wasu mutane ayyukan gona a wasu gonakin.
“Esther ta kira ni daga inda nake koyon sana’ar dinki don in zo na karbi kudina na man gyada da nake bin mijinta. Saboda bayan sayar da mai da nake yi ina yin wa wasu mutane mutane aikin gona a wasu garuruwa.
“Na yi gaggawar ficewa daga shagon ogana, ban san cewa ta yi kira ne don kawai na je ta watsa min ruwan zafi akan laifin da ban aikata ba,” in ji ta.
Shi ma mijin wanda ake zargin, Godwin, ya musanta zargin alakanta shi da aka yi da wacce aka watsa wa ruwan zafin na cewa suna aikata alfahsha.
“Ni ne nake biyan kudin jinyar wanda abin ya shafa a asibiti tun da abin ya faru har zuwa yau,” in ji shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta ce wacce ake zargin a halin yanzu dai ba ta hannun ‘yansanda, domin tuni maganar ta kai ga kotu.
“An gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu, ba ta tare da mu,” in ji PPRO.