ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno

by Sadiq
1 year ago
Boko Haram

Aƙalla mutane 12 ne ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kashe a ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno.

Mai Martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya shaida wa LEADERSHIP cewa ‘yan ƙungiyar sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) guda biyu sun rasa ransu a harin kwanton-ɓauna a kan hanyar Kirawa a ranar Juma’a, 25 ga watan Afrilu, 2025.

  • Yadda Sakamakon Jawo Jarin Waje A Rubu’in Farko Na Bana Ya Ba Da Sha’awa A Kasar Sin
  • Zulum Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Boko Haram Ke Dawowa Wasu Yankuna A Borno

A ranar Asabar, 26 ga watan Afrilu, wasu mutane 10 da suka je yin itacen girki a daji an kashe su a ƙauyen Bokko Ghide.

ADVERTISEMENT

Wasu biyu kuma sun ji rauni sosai a harin.

Sarkin ya bayyana takaicinsa kan yawaitar hare-hare, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Borno da sojoji ke yi na sake gina yankuna da kuma dawo da ‘yan gudun hijira gida.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

“Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau.

“Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in ji Sarkin.

Ya yi addu’a Allah ya jiƙan mamatan ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.

Sarkin ya yaba wa gwamnati da sojoji bisa ƙoƙarinsu amma ya buƙaci a ƙara amfani da sabbin fasahohin zamani da kayan yaki masu ƙarfi domin yaƙar ‘yan ta’addan.

Ya yi gargaɗin cewa waɗannan hare-hare na iya tsoratar da manoma wajen komawa gonakinsu yayin da lokacin shuka ke gabatowa.

A wani ɓangare kuma, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sake kira ga rundunar soji da su ɗauki mataki wajen fatattakar ‘yan Boko Haram daga maɓoyarsu.

Gwamna Zulum ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, da sauran manyan hafsoshin soji a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri.

MASU ALAKA

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027
Labarai

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Siyasa

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026
Next Post
Sin Ta Gina Cibiyoyin Fasahar Aikin Gona Na Gwaji Guda 24 A Afirka

Muhimman Dalilan Kirkiro Da Shirin Inganta Aikin Noma ‘SAPZ’

LABARAI MASU NASABA

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026
Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

July 16, 2026
Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

July 16, 2026
Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.