Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau sakon wata baiwar Allah ce wanda ta aiko, inda ta bukaci a sakaya sunanta. Baya ga haka ta nemi shawarar mabiya shafin Taskira. Inda sakon nata ya fara da cewa:
“Don Allah ina so ku ba ni shawara kan wannan abin da ya dame ni sosai. Budurwar mijina ce ta yi aure, to wallahi tun lokacin ya fita hayyacinsa ya shiga damuwa, ya rame, kowa ya ganshi sai ya tambaye shi ‘wane lafiya kuwa kana ta ramewa?’ Wallahi gaba daya ya canza! Na rasa gane masa ko kusa da shi na matsa sai ya ce; in ba shi wuri don kar na dame shi. Kuma bai san na sani ba, yana boye mun, ko gun kwanciya idan na zo na kwanta sai ya ce in tashi kar in takura masa, haka zai sa wakokin rabuwa yana saurare, yanzu su ne abokan hirar shi.
Wallahi ina cikin damuwa yanzu haka da nake wannan rubutun kuka nake, gaba daya ba na gabanshi, ya dauki damuwa ya sa wa ranshi. Idan na tambaye shi, ‘wane me ke damun ka na ga duk ka canzam’ sai ya ce min ‘ba komai’, alhali bai san na san komai ba. Yanzu in nuna masa na sani ne ko dai in kyale shi in ga iya gudun ruwansa? Amma dai ina cutuwa gaskiya. Don Allah ku ba ni shawara, me ya kamata na yi? Ya zan bullo wa lamarin?”.
Ga kuma shawarwarin mabiya shafin kamar haka:
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta Kaura-Namoda Jihar Zamfara:
Kafin na ce komai zan ce da ke ki yi hakuri, saboda shi ne mataki na farko da za zan fara dora ki a kai. Saboda ita kalmar hakuri, a duk lokacin da kika ji an ce da mutum ya yi shi, an cutar da shi. Sai dai ke naki hakurin ya sha bamban da saura, domin babu mai iya kwatanta yadda kike ji face wanda ya dandani irin zafin da kike ji a cikin zuciyarki.
Don haka ki yi hakuri, ki kara danne zuciyarki a kan duk abin da za ki gani dangane da wannan matsalar. Saboda shi kansa ba yin kansa ba ne, jarabta ce ta Allah kwatankwacin wacce kike ciki. Ki daga masa kafa, ki sakar masa rata, kuma ki ja fili tsakaninki da shi matukar ba rarrashinsa za ki yi ba. Amma muddin kika ce za ki zafafa a daidai wannan lokacin da yake ciki; ba fata ake yi ba, amma abin da zai biyo baya ba mai dadi ba ne. Saboda haka cikin hikima irin tamu ta mata, ki yi kokarin janyo abinki a jiki, ta hanyoyin da kika san ba zai ga kamar kin takura masa ba. Ubangiji ya kawo miki mafita a cikin al’amurranki gaba daya, domin so masifa ne, rabuwa bala’i ce, wacce zafinta ya fi kowane irin zafi kuna a cikin zuciya.
Wanda idan ba Allah ya tsare ba zuciya tana iya bugawa a daidai a irin wannan lokacin. Amma kalamai masu dadi, kulawa, tarairaya cikin hikima duka suna warkar da ciwon ba tare da an tantance ba. Ki yi kokarin tausar kanki ki damu da damuwar mijinki. Allah ya kara muku zaman lafiya da fahimtar juna..
Sunana Zarah Muhammad Sunusi (Ummu Heebbat) daga Gaidam:
To da farko dai ta zama mai yin addu’a, kuma dukkan sanda za ta yi addu’ar ta fara fadin “La’ilaha illa anta subuhanaka inni kuntu minazzalimin”. Wannan kalmar dukkan addu’ar da mutum zai yi da iklasi matukar zai yi ta ya karanta haka ya roki Allah, in sha Allahu Allah zai amsa masa. A bangare na gaba kuma shi ne; ni dai a nawa tunanin, kawai ta same shi idan yana hutawa ta ajiiye ma shi abu mai sanyi ko bai kallah ba ta daure zuciyarta ta ce. ”Mijina wallahi ina sonka amma na gaza gane kanka, wannan yarinya idan har Alkairi ce cikin rayuwar ka Allah ya sa da rabon aure tsakaninku. Hakika na taya ka bakin cikin rashinta, saboda dukkan wanda ya rasa abin da yake so dole ya shiga wani hali, kamar yadda na shiga a yanzu duk da cewa ba ni ce gabanka ba, amma wallahi ina matukar kaunarka kuma ina kaunar abin da ka ke kauna.” Abin fa sai an daure gaskiya saboda gudun mala’ikun Amin su ce amin. In sha Allahu matukar yana kaunarki da can baya kuma kuna zaman lafiya wallahi zai ji tausayinki kuma zai ji kunyarki ta mamaye shi. Ko da bai baki amsa ba, zai rage in sha Allahu. Allah ya sa mu dace .
Sunana Lawan Isma’il (Abu Amfusamu) daga Jihar Kano Yalwa Nada:
Da farko addu’a ita ce kan gaba ko da a cikin sujadar sallar farilla ne tana saka bukatarta dama sauran al’umma, sannan ta sami koda kwana 7 ne tana sallar dare akan wannan bukatar ta ta in sha Allahu komai zai warware cikin sauki. Sannan a tsawon zamansu da shi mijin nata na san ba za ta manta abin da take yi masa yake jin dadinsa ba, sannan da kalar abinci ko na sha wanda ya fi so to koda kudinta ne tayi masa wannan indai har ya zo amfani da wannan abin sha din ko na ci sai ta san irin kisisinar da take yi masa take jan hankalinsa to tananma in sha Allahu za ta rinka kara kwamtar masa da hankali har ya sakko ya sami nutsuwa.
Sannan ya ma mance da waccan in sha Allah, amma gaskiya kada tayi tunanin hada shi da wani nasa ita ya kamata tayi kokarin ganin janyo hankalinsa.
Sunana Kueen Nasmah daga Jihar Zamfara:
To baiwar Allah, ita dai rayuwar nan kowa da irin ta shi Jarabawar, ta iya yuwuwa ta wannan hanyar Mahaliccinmu yake son gwada imaninki. Amma ki yi hakuri ki kuma jajirce, kar ki cire rai. Ki je ki same shi, ki mishi magana cikin hikima da nuna soyayya, ki kara da nuna mishi kin fahimci komai abin da ke damunsa, amma ba damuwa ya kamata ace yayi ba addu’a ya kamata a ce yana yi.ki dage da addu’o’i kuma, da sallar nafila.
Sunana Aisha Adamu Alhassan:
A iya tunanina wannan a wurinta ba wani abun damuwa ba ne, duba da yadda bawa ke riskar kanshi cikin irin wannan yanayin. Magana ta gaskiya tayi hakuri ta daina kuka don komai lokaci ne babu abin dawwama, rabuwa babu dadi tunda har ta san cewa ga a mizanin da yake da budurwa, kamata ya yi ta kau da kai gefe tai hakuri abun na dan wani lokaci ne. Ita fa shakuwa wata aba ce wacce sai dai mutum ya yi hakuri ya yi rabuwa don wani abun sai dai kiyayewar Ubangiji.
Sunana Faridat Hussain Mshelia (Ummu-jidda):
Hakuri tare da addu’a su ne babban matakin da za ki rika sister, tunda har tayi aure ai kishi da soyayyarta ma ya kare, kin san halin mijinki kin san kuma a wani irin nau’in mazaje yake, idan ya kasance wanda ku ke zama ku tattauna Matsala har a samu mafita sai ki tunkare shi cikin nutsuwa da tausasa harshe, ki ba shi hakuri sosai tare da zayyano mishi ayoyin kaddara idan kuma ya kasance akasin haka sai ki sa juriya har ya sauka dan kanshi, ka da ki yarda damuwar shi ta miki illa dan haka ki hana idanuwanki bacci cikin dare ki sanar wa Ubangiji bukatar ki, Allah ya kara miki hakuri da juriya.
Sunana Zee MD:
Shawarar da zan baki ita ce “kiyi hakuri ki daina damuwa da hakan, ki kasance me hakuri da shi zuwa wani lokacin, tabbas da ciwo ka ga Masoyinka na cikin damuwa kuma ka kasa magance Masa ita. Ki yi kokarin faranta masa ta hanyoyin da kika san yana so, duk abin da ki ka san yana so ki kasance mai yi masa, hakan zai sa zuciyarsa ta dunga sanyi har zuwa lokacin da alhinin rabuwa da ita zai sake shi. Sannan ki kasance me yawan yi masa addu’a in sha Allah zai samu sassauci da nutsuwa, tabbas rabuwa da masoyi akwai ciwo amman in kasa dangana da hakuri tare da mika lamuranka ga Allah to komai zai zo da sauki. Allah kasa mu dace ka hadamu da masoyanmu na gaskiya, Ameen.
Sunana Zahra’u Abubakar (Dr. Zarah) daga Jihar Kano Karamar Hukumar Nassarawa Gama-D:
‘Yar uwa muna miki fatan alkhairi Allah ya shigo cikin lamuranki, ya daidai ta ki da mijinki. Shawarar da zan baki ki ci gaba da hakuri da halin da kike ciki tunda har Allah ya sa kin san dalili sai ki ci gaba da fadawa Allah ki dage da addu’a sosai Allah ya yaye masa damuwarsa Allah ya mantar da shi ita a cikin zuciyarsa. Sannan ba ja da baya za ki yi da shi ba in ya ce ki tafi kar ki dame shi, salo za ki fito da su kala-kala ki nuna masa kin san budurwarsa tayi aure, amma ba farin ciki kike da hakan ba, ke ma kin damu daga nan zai rage sosai ya dawo saurarar ki, ki nuna masa kina yi masa fatan ya samu wata wacce ta fita, wannan sauraran wakokin rabuwar da yake yi ki sa ya janye a hankali ki nuna masa sauraran karatun alkur’an ya fi masa sauraran wannan wakokin a hankali sai ki ga komai ya koma daidai ki dage da kwalliya da tsabta da girke-girke masu dadi musanman irin wanda yake so Allah ya daidaita ku ‘yar uwa.
Sunana Haleema Kabeer (Nana Haleema) daga Jihar Kano:
Addu’a ita ce abin da ya kama ce ki ki rike babu dare babu rana, domin ko shi da yake cikin yanayin da zai rike addu’a komai sai ya manta da shi balle ke da kike neman mafita aka kuma cutar dake akan abin da ba laifinki ba. ‘Yar uwa ki kama addu’a koda kin ganshi cikin wannan yanayin kada ya dame ki ki kawar da kanki kar dai ki daina kula da mijinki sabida wannan abun, ki daure ki kawar ki ci gaba da rokon Allah komai zai zo ya wuce kamar ba a yi ba amma tabbas sai kin daure.
Lamarin babu dadi amma in kika kama addu’a komai za ki manta da shi shi ma kuma ki dinga yi masa domin ya fita daga damuwa karuwarki ce zaman sa cikin damuwa tauyewarki ce.
Magana mai sanyi babu fada a cikin maganarki ki dinga tausasa harshe in ba haka ba yadda yake cikin wannan yanayin abu kadan zai iya hasala shi karshe a zo garin neman gira a rasa idanu.