Ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin ta sanar a ranar Alhamis cewa, Sin da Amurka sun yi tattaunawa kan tinkarar sauyin yanayi a birnin Beijing.
Wakilin musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua da takwaransa na Amurka John Kerry sun gana a birnin Beijing, inda suka yi musayar ra’ayi kan aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron da suka yi a birnin Bali na kasar Indonesiya, game da tinkarar sauyin yanayi tare.
Bangarorin biyu sun zurfafa tattaunawa ta gaskiya kan aiwatar da sanarwar da Sin da Amurka suka fitar tare don magance rikicin sauyin yanayi da Sanarwar Sin da Amurka ta Glasgow kan Habaka Ayyukan Daidaita Yanayi ta shekara 2020. (Yahaya Babs)