Wani jami’in kasar Sin ya bayyana a jiya cewa, tsarin babban taron wakilan jama’ar kasar Sin, muhimmin mataki ne dake tabbatar da tsarin dimokuradiyyar da ya shafi matakai baki daya, kana wani dandali dake da tabbatar da damawa da kowa yadda ya kamata.
Darektan ofishin bincike na babban ofishin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Song Rui ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka shirya, kan ci gaba da nasarorin da aka samu, wajen tabbatar da kyautata tsarin babban taron wakilan jama’ar kasar a sabon zamani.
Dangane da kyautata tsarin kuwa, Song ya yi nuni da cewa, abu mai muhummaci da ya kamata al’umma su kasance a matsayinsu na masu rike da madafun iko a kasa, shi ne rikewa da gudanar da mulkin kasa yadda ya kamata, ta hanyar babban taron wakilan jama’a wajen tafiyar da harkokin kasa.
Ya ce, babban taron wakilan jama’a a dukkan matakai, su ne ginshikan da ke tabbatar da cewa, jama’a suna tafiyar da harkokin kasa, ta hanyar tafiyar da al’amuran zamantakewa da tattalin arziki da al’adu bisa tanadin doka.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp