Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, gwamnatin na aiki tukuru wajen samar da shirye-shirye da za su rage musu radadin tsadar farashin man fetur da ake fama da shi.
Tun bayan cire tallafin mai, ana kuma ci gaba da samun karin hauhawar farashin kayan masarufi a daukacin fadin Nijeriya.
Man fetur wanda a baya ake sayar da Lita daya kan kimanin Naira 190 amma a yanzu ya ninka zuwa daga Naira 600 zuwa 700 tun bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man.
‘Yan Nijeriya da dama dai, sun soki wannan matakin na gwamnatin tarayya, amma Akume ya ce, gwamnatin na kan daukar matakan da za ta rage wa ‘yan Nijeriya radadin da suke ji na hauhawar farashin kayan masarufi.
Sakataren wanda ya bayyana hakan sanar da hakan a shafinsa na Twitter ya ce, gwamnatin ta ji koke-koken da ‘yan Nijeriya ke yi kuma ta na kan aiki don lalubo da mafita kan lamarin, inda ya roki ‘yan kasar da su ci gaba da hakuri.