Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Caroline Wura-Ola Adepoju, ta samar wa ma’aikatan hukumar motocin sufuri don rage musu radadin karin kudin sufuri da aka samu.
Wannan na zuwa ne bayan karin farashin sufuri da aka yi a baya-bayan nan sakamakon cire tallafin man fetur.
- Ministar Ghana Ta Yi Murabus Bayan Sace Makudaden Kudade A Gidanta
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Boko Haram Kan Zargin Shirin Kai Hari Gidan Atiku
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hukumar, Kenneth Kure da ya fitar a ranar Litinin.
Ta dauki wani ne mataki don saukaka wa ma’aikatan NIS ta hanyar gabatar da jerin motocin bas don bukatunsu na sufuri.
Wannan wani bangare ne na tsare-tsarenta don walwala da kuma nufin inganta rayuwar ma’aikatan hukumar.
A wani takaitaccen biki da aka gudanar a hedikwatar NIS da ke Abuja, a ranar Litinin 24 ga watan Yuli, 2023, mukaddashiyar ta mika motocin bas din a hukumance ga jami’an hukumar.
A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tallafawa da inganta walwalar ma’aikata, inda ta nuna muhimmancin aikinsu da kuma sadaukarwar da suke yi wa wannan kasa.
“Ana sa ran samar da wadannan motocin bas din zai gyara kalubalen kudi da aka samu sakamakon karin kudin sufuri da aka samu a baya-bayan nan da kuma tabbatar da samar da sauki ga ma’aikatanmu,” in ji ta.
Mukaddashiyar ta bayyana cewa an riga an sayo karin motocin bas da za su ke bi manyan hanyoyin Abuja don jigilar ma’aikatan hukumar.
Ta kuma bayyana kudurinta na fadada wannan tsari ga sauran hukumomin jihohin kasar nan.
Caroline Wura-Ola Adepoju, ta shawarci direbobin motocin da su nuna kwazo wajen gudanar da ayyukansu.
Ta kuma jaddada muhimmancin bin ka’idojin tuki na tafiya a kan kilomita 60 duk cikin sa’a guda, tare da tabbatar da tsaron ma’aikatan yayin jigilarsu.
Har wa yau, ta yi kira ga daukacin jami’an hukumar da su dauki nauyin kula da bas din da aka tanadar domim su yadda ya kamata.
Ta kara da cewa “Wannan kokarin hadin gwiwa zai tabbatar da dadewar motocin tare da bai wa NIS damar dorewar wannan shiri mai.”