Shugaban kasar Benin Patrice Talon ya iso fadar shugaban kasa da ke Abuja domin ganawa da shugaba Bola Tinubu.
Ziyarar dai ita ce karo ta biyu da shugaba Talon ya kai Abuja cikin kwanaki tara, a ranar 18 ga watan Yuli tare da rakiyar wasu takwarorinsa biyu, shugaba Mohamed Bazoum na jamhuriyar Nijar da shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea-Bissau.
Ganawar gaggawar ta samo asali ne kan tsare shugaba Bazoum na kasar Nijar da wasu dakarun tsaron fadar shugaban kasar suka yi, wadanda a halin yanzu ke fuskantar turjiya daga manyan Sojojin kasar.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, Tinubu shi ne sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS).