A wani yunkuri na dakile yajin aikin da kungiyar kwadago ke shirin fara wa a fadin Nijeriya, Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ma’aikata a kasar da su dan dakata su ba gwamnatinsa karin lokaci don biyan bukatunsu.
Shugaban majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abass, wanda ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar domin ganawa da shugaba Tinubu a ranar Laraba ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi gargadin cewa, ma’aikata a kasar za su gudanar da zanga-zanga na tsawon mako guda domin nuna rashin amincewarsu da karin farashin man fetur na baya-bayan nan.
“A wani bangare na nauyin da ya rataya a wuyanmu, Majalisar Wakilai ta bayyana shirinta na shiga tsakanin gwamnati da ma’aikata kan zanga-zangar da NLC ke shirin yi, wadda za ta fara daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta.” Inji Tajudeen