Shugaban hukumar kula da ilimin bai-daya na Jihar Katsina, Da Kabir Magaji ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Katsina za ta dauki malamai aiki a manyan makarantu.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mahukuntan kwalejin Isah Kaita da ke Dutsinma da suka kai masa ziyarar taya shi murna a ofishinsa.
Dakta Magaji ya bayyana bukatar da ke akwai na gwamnati ta lura da malaman wadanda suka yi karanci a fadin jihar, inda ya yi ce kamata ya yi kowane darasi da yana da malami guda da ke karangtar da shi a manyan makarantun gwamnati.
Shugaban hukumar ya kara da cewa, hukumar za ta yi bakin kokarinta na horar da malamai, sannan ya bukaci goyon bayan kwalejin.
Tun da farko, shugaban kwalejin, Dakta Ismaila Ado Funtua, ya ce sun zo ofishin shugaban hukumar bayar da ilimin bai-daya domin nuna sanayyar a ma’aikatan da kuma taya shi murnar samun aiki da aka ba shi a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ilimin bai-daya ta jiha.
Ya yi addu’a Allah ya taimaka wa gwamna Malam Dikko Radda a kan damar da ya samu na shugabancin jihar da kuma kai ilimi a wani babban mataki.
Shugaban kwalejin ya yi kira ga shugaban hukumar da ya ci gaba da hadin gwiwa da kwalejin domin samun ci gaban ilimi da kuma samar da ingantanccen koyo da koyarwa a jihar.