A makon da ya gabata ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya mika sunayen ministoci 28, ban da wasu jihohi 11 ciki har da Kano.
Wata majiya ta bayyana wa NIGERIA TRACKER cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya dage kan mika sunan, Injiniya Rabi’u Suleiman Bichi daga Kano.
- Ganduje Ya Aike Da Sunan Gawuna A Masa Mukamin Minista
- Dalilin Da Ya Sa Tinubu Bai Bawa Kano Mukamin Minista Ba
Sai dai kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, shi ma yana matsa lamba kan a saka sunansa cikin jerin sunayen da za a mikawa majalisar dattawa domin tantancewa.
Majiyar ta kara da cewa a yanzu dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC ya aike da wasu wakilansa zuwa wajen Gwamna Ganduje, inda suka bukace shi da ya mika sunan Gawunan a matsayin minista daga Kano.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa, Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya yi alkawarin ba wa Kano mukaman minista guda biyu, daya daga tsagin Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da daya kuma daga tsagin Jagoran Gandujiyya kuma tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Tun da Ganduje ba zai samu shiga cikin kunshin ministocin Shugaba Tinubu ba, shugaban kasar ya ba shi damar kawo minista, wanda a yanzu haka ya janyo cece-kuce a da’irar siyasar tsohon Gwamna Ganduje.
Majiyar ta kuma sanar da NIGERIAN TRACKER cewa idan shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya mika sunayen ministoci na gaba daga Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma wani mutum daya daga tsagin Ganduje ne da ya mika.
Wata majiya ta ce, tsagin rusasshiyar jam’iyyar ACN a Kano, karkashin jagorancin shugaba Tinubu a zabukan 2007 da 2011, na matse lamba wajen nada dan takarar gwamna na jam’iyyar a 2011 kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano. Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo.
Dalilan da tsaffin jiga-jigan jam’iyyar ACN suka bayar na cewa shugaba Tinubu ya nada ATM Gwarzo a cikin majalisarsa, shi ne, shugaba Tinubu ya yi fice wajen bayar da ladan siyasa, kuma kasancewarsa amininsa na tuntuni, don haka Injiniya Gwarzo yana cikin wadanda suka fi cancantar zama minista a Kano.
Don haka ana sa ran shugaba Tinubu zai tuntubi tsagin tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, duk da cewa a halin yanzu yana PDP, saboda rawar da ya taka wajen kafa APC a 2011.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu ba shi da gaggawar nada ministoci daga Kano, don akwai yuyuwar kafin nadin ministocin zai tuntubi Sarkin Kano na 14, kafin ya mika sunayen daga Kano.