Majalisar Dattawa ta umarci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kammala gina Makaratar Horas da Jami’an Hana Fasakwauri ta Kasa wato Kwastom da ke Jihar Bauchi don inganta samar da jami’ai kwararru da za su kawo gyara da ci gaba a kasar nan.
Majalisar ta bayar da wannan umarni ne ran Alhamis a lokacin da Sanata Mai Wakiltar Bauchi ta Kudu, Sanata Buba Umar Shehu ya gabatar da bukata ta musamman a gaban Majalisar.
Sanata Buba ya ce dalilin gabatar da wannan kuduri shi ne ya lura cewa an saka ginin wannan makaranta a cikin kasafin Kudi na shekara ta 2023 in da za a kashe kimanin kudi sama da Naira Biliyan 14 amma har ya zuwa yanzu shekara ta raba ba a yi komai akan gina makarantar ba.
Ya ce gina wannan makaranta zai kawo gagaramin ci gaba ga kasa baki daya ta hanyar samar da horo ga jami’an Hana Fasa Kwauri wanda zai yi sanadiyar kawo ci gaba ta fannin samar da kudin shiga da kwarewa da kawar da barna a gurare da dama a kasar nan.
Kudurin nasa wanda ya sami goyan bayan dukkanin Sanatocin Majalisar in da suka bayar da gudunmawa wajen ganin an ja hankalin gwamnatin Tarayya ta gaggauta ganin an samar da makarantar don amfanar ‘Yan Nijeriya.
Sanata Buba ya ce yana da kwarin gwiwa cewa Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai bayar da umarni ba tare da bata lokaci ba wajen ganin an kammala makarantar sabo da muhimmancin ta ga kasa ta fannin tsaro da samar da kudaden shiga.
A wani bangaren kuma, Sanata Buba ya sha alwashin ganin an samar da ingantaccen tsaro a kasar nan ta hanyar tattaunawa da jami’an tsaro a kai a kai a matsayin sa na shugaban Kwamitin da aka kafa a Majalisar akan fannin Tsaro.
Ya ce tsaro shi ne ginshikin duk wani ci gaba sabo da haka ne ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samar da ingantaccen tsaro a kasarnan.
A hirarsa da ‘Yan Jaridu a ofishinsa, Sanata Buba ya yi kira da ‘Yan Nijeriya da su ba wa Jami’an tsaro hadin kai wajen ganin an samar da tsaro mai inganci a kasarnan. In da ya kara da cewa hakki ne da ya dogara a kan kowa tun da ba wanda zai magance mana barazanar tsaro a kasar nan sai mu da kammu mun hada gwiwa da jami’an tsaro.
A bangaren Ministoci da aka gabatar da sunayensu ranar Alhamis, ya yaba wa kokarin Shugaban Kasa na ganin ya gabatar da sunayen kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukata.
Daga karshe dan majalisar ya yi kira da ‘Yan Nijeriya musamman wadanda ba a fadi sunayen Ministoci da ke Jihohin su ba da su kara hakuri cewa shugaban kasa ya yi alkawari gabatar da sauran sunayen watakila kafin a gama tantance sunayen wadanda aka gabatar.